GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

2019: Hon. Abdullahi Yayi Kira Ga Hadin Kan Mambobin Jam’iyyar APC Don Samun Nasara A Lokacin Zabe

2019: Hon. Abdullahi Yayi Kira Ga Hadin Kan Mambobin Jam'iyyar APC Don Samun Nasara A Lokacin Zabe

65

- Advertisement -

Dan majalisan wakilai na kasar Nijeriya mai wakiltar mazabar Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu a jihar Neja, Hon. Abdullahi Idris Garba (Mai Solar), yayi kira ga mambobin jam’iyyar APC da ke karkashin mazabarsa da ma Nijeriya ga baki daya da su hada kansu wajen ganin cewa jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2019.

Karanta wannan: Yadda Shugaba Buhari Ya Taimaka Min Wajen Zaben Mataimakiya: El-Rufa’i

Dan majalisan yayi wannan bayanin ne a yayin da ya ke magana da wakilinmu a wayar tarho.

Karanta wannan: Kotu Ta Yankewa Matashi Hukuncin Kisa Ta Hanyar Kisa

Hon. Abdullahi Idris Garba (Mai Solar) ya bayyana cewa yana nan a kan bakansa na wajen ganin cewa jam’iyyar ta samu ci gaba a jihar da kasa ga baki daya tare da samarwa al’ummar mazabarsa ci gaba ta hanyar gudanar masu ayyukan da ya kamata domin moriyar rayuwa.

Karanta wannan: An Gano Wata ‘Yar Shekaru 12 Wacce ‘Yan Bindiga Suka Sace A Ilorin A Jihar Ekiti

A karkashe, dan majalisan yayi kira ga duk mambobin jam’iyyar da su kauracewa rikicin zabe.

Leave A Reply

Your email address will not be published.