GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ki Kiyaye Domin Samun Lafiyayyen Farji

Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ki Kiyaye Domin Samun Lafiyayyen Farji

278

- Advertisement -

Farjin mace na daya na jikinta da za ka iya kira da kayan aras ko fadi ka mutu. Ma’ana dai wannan eriya da sau tari su matan kan kira da “Headquarters” (hedikwata) kamar dai tangaran ne, sai an ririta shi, an bashi kulawa ta musamman, an ki yi masa rikon sakainar kashi, domin da zarar ya fadi, fashewa zai yi kuma ba zai sake dawowa yadda ya ke ba.

 

 

Wannan dalili e ma ya sanya masana kiwon lafiyar sassan jiki suke kira ga mata da su baiwa wannan bangare na jiki kula mai inganci domin in ya tabu, ya tabu kenan har abada in ba sa’a aka yi ba

 

 

Sai dai wajen kokari baiwa farji kulawa, mata na aikata wasu abubuwa da a maimakon ya samar wajen kariya ta din-din-din, a’a, sai ma ya kasance su haifawa wajen wata matsala ko dai ta wucin gadi ko kuma matsala ta din-din-din

 

Karanta Wannan: Takai Ya Yi Watsi Da Jita-Jitar Da Ake Yaɗawa Cewa Ya Ce A Marawa Abba Kabir Na PDP Baya

 

Ga jerin dabi’un da mata ke yi da ka iya haddasa musu wata fitinar a hedikwata:

  • Sanya damamman dan kanfai kullum: Sanya dan kanfai abu ne mai kyau ko ga lafiyar farji ma, amma sanya shi kullum shi ne matsala domin yin haka zai iya haifar da kwayoyin halittar bakteriya da ka iya cutar da farjin. In har ya zame miki dole sai kin saka dan kanfai, to ki kiyaye sauya wanda ke jikinki duk bayan awanni 4

 

  • Dumama farji: Wasu da dama na da dabi’ar nan na yin amfani da ruwan dumi ko kuma turiri wajen dumama farji. Ko shakka babu wannan dabi’a na da matukar hatsari ga lafiyar farji duk kuwa da cewa wasu na da ra’ayin cewa dumama farji ga ‘yan mata na kawo saukin ciwon fitar al’ada

 

Karanta: Ba Zan Bar Abba Kabiru Yusuf Ya Biya Mafi Ƙarancin Albashi Ba – Inji Kwankwaso

 

  • Kuskure Wajen Tsarki: Fa mata masu yin amfani da takardar goge al’aura bayan sun yi tsarki ya kamata ku sani cewa ba a gogewa daga baya (dubura) zuwa gaba (farji), domin dubara na dauke da kwayoyin cuta da a kowane lokaci suna nan. Saboda haka gogowa daga baya zuwa gaba na iya dauko wadannan kwayoyin cuta daga dubura zuwa farji

 

  • Kwana da Dan Kanfai: A duk lokacin da za ki kwanta bacci, to ki cire dan kanfanki in ba dai kina al’ada bane a lokacin. Kwanciya da dan kanfai na hana farji numfasawa yadda ya kamata, inda hakan zai iya haifar da kwayoyin cutar da za iya kawowa hedikwata matsala ko matsaloli daban-daban. Wani lokaci za ki kawai gabanki ya fara miki kaikayi, kina susa a duk dan kankanin lokaci, wani lokaci kuma ki ji kin bushe babu alamar danshi a gabanki da ya kamata a ce akwai a kowane lokaci. Wadannan ko shakka babu ‘yan kura-kuran da ake yi ne ke haifar da su

 

Karanta: Every-Woman: Kadan Daga Cikin Falalar Zama Da Mace Daya

 

  • Fesa Turare a Farji: Fesa turare a farji ko kusa da farji ko da kuwa akan dan kanfanki ne babban kuskurene. Babu wani dalili da zai saka ki yin hakan. Duk wata hanya ta yi wa farji turare, ko ta hanyar hayaki ko ta fesawa kuskure ne kaulan wahidan

Leave A Reply

Your email address will not be published.