GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Aisha Buhari Ta Sake Nuna Rashin Jin Dadinta A Kan Tafiyar Da Gwamnatin Mijinta

Aisha Buhari Ta Sake Nuna Rashin Jin Dadinta A Kan Tafiyar Da Gwamnatin Mijinta

149

- Advertisement -

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bayyana rashin jin dadinta dangane da yadda ake nuna rashin gaskiya wajen tafiyar da harkokin gwamnati, musamman wadanda suka shafi rayuwar mata da talakawa.

 

Karanta: An Sace Mutane Sama Da 30 A Kwanaki Biyu Kacal A Hanyar Kaduna-Abuja

 

Uwargidan shugaban kasar ta koka ne a yayin wani taron mata da ta kira a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda ta caccaki Babbar Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara kan shirin yaki da kuncin rayuwa na Social Investment Programme (SIP) Hajiya Maryam Uwais, game da yadda take gudanar da shirin wanda yake lakume makudan kudade da sunan tallafawa matan karkara da masu kananan sana’o’i. Ta ce, shirin bai yi wani tasirin a zo a gani ba a jihohin Arewa, musamman jiharta ta Adamawa, inda Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) Boss Gida Mustapha ya fito.

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana cewa, mata 30,000 daga Jihar Adamawa, wadanda za a bai wa tallafin Naira dubu 10 kowaccensu, ya kamata su amfana da wannan tallafin, amma har yanzu da zangon farko na shugaban ke dab da karewa, babu wani labari mai dadi.

A cewar ta, ban san wata jiha a Arewa da ta amfana da wannan shiri ba, mai yiwuwa wasu sun samu, amma wadanda aka yi abin domin su ba su san ana yi ba har yanzu. A jihata ta Adamawa, karamar hukuma daya ce kawai aka kaddamar da shirin, amma sauran 22 din babu wani bayani. Ban san ko haka abin yake a Kano ba.

Ta ci gaba da cewa, muna da mata da yawa a Arewa da ke tsananin bukatar irin wannan tallafin, don su fadada kasuwancinsu, wadanda akasari a cikin gidajensu na aure suke yi, saboda dalilai na al’ada. Yawancin matan Arewa ba sa iya kafa kungiya da sunan kasuwanci, ya kamata a bullo mu su da wani tsari ta yadda su ma za su ci moriyar tanadin da gwamnati ta yi mu su.

Uwargidan shugaban kasar ta yi nuni da yadda sakaci da rashin gaskiya suke lalata manufofin gwamnati ta yadda ba sa isa ga wadanda aka yi tanadi dominsu, wanda dalilin haka za a yi ta sukar gwamnati da rashin damuwa da rayuwar talakawanta. Alhalin wadanda aka bai wa alhakin gudanar da ayyukan ne ba su yi abin da ya kamata ba.

Ta ce, ban cika son ina magana sosai kan yadda ake tafiyar da wasu abubuwan ba, don wasu na ganin ina da yawan korafi, amma wasu abubuwan ba zai yiwu a kawar da kai daga kansu ba.

Aisha Buhari ta kuma bayyana takaicinta game da wasu kudade da Gwamnatin Tarayya ta fitar da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 16, a matsayin kudin karo karo don yaki da cutar maleriya, amma sai aka ce an yi amfani da su wajen sayen gidajen sauro da za a rabawa mutane, alhalin wannan kudin kansa ya ci a ce an yi feshin magani kusan a dukkan kasar nan, domin kawar da yaduwar sauro baki daya.

A cewarta, ni kaina da na nemi a bani nawa kason don rabawa ga mutanen garinmu, ban samu ba. Ballantana sauran mata da ke kauyuka da lunguna cikin karkara.Har wa yau, uwargidan shugaban kasa ta fallasa batun wasu kudade da ta ce sun kai Naira biliyan 12 da shugaban kasa ya bayar, domin kula da mutanen da suka tagayyara kuma rayuwarsu ke fuskantar kalubalen lafiyar kwakwalwa.

‘Ya kamata lallai a sa ido don sanin yadda aka yi da kudaden. Nan ba da dadewa ba, ministoci za su tafi, kuma kudin nan an riga an fitar da shi,’ in ji Aisha.

 

Karanta: Facebook Na Shirin Fito Fa Hanyar Da Mutane Za Su Gane Masu Sonsu A Boye

 

A yayin da take yabawa Sakataren Gwamnatin Tarayya game da shigar da mata cikin hidimar bikin rantsar da sabuwar gwamnati zango na biyu, Aisha Buhari ta kuma roki shugabannin jam’iyyar APC su mayar wa da mata ‘yan siyasa kudaden da suka biya wajen neman izinin tsayawa takara a babban zaben 2019. Ta shawarci mata su tashi tsaye wajen ganin sun cimma muradunsu tare da alkawarin cigaba da kokarin kare hakkokinsu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.