GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Alamomin Ciwon Daji Na Nono (Sankarn Mama) ‘Breast Cancer’

Alamomin Ciwon Daji Na Nono (Sankarn Mama) 'Breast Cancer'

653

- Advertisement -

Ciwon dajin nono, ciwo ne mai lahani da illa ga rayiwar bil’adama mussan mata, ko da yake su Kansu mazan na kamuwa da ciwon dajin nono nan, amma ba kasafai ba.

Bazuwar sa:

Acikin mata takwas (8) a kan samu daya na dauke da ciwon bayan anyi gwaji. Maza kuwa a iya cewa daya cikin hamsin (50). Maza ma na iya kamuwa da ciwon saboda wasu irin tarin hallitun jini (tissues) dake cikin kokwan nonon nasu ko da yake yana da kankanta.

 

Karanta: Tirr! Wata Matar Aure Tare Da Kwarton Ta Sun Makale A Yayin Da Suke Jima’i (Bidiyo)

 

A shekaru nawa mace ka iya kamuwa da ciwon?
Mafi yawan masu dauke da ciwon na kamuwa dashi ne a shekarun 50 zuwa 60. Amma su ma yan matan kan kankama su. Saboda haka ne yasa kwanaki na kawo muku hanyoyin rigakafin kamuwa da wannan cuta.

Ya cutar dajin nono ke fara habaka?

Cutar na fara haka ne a yayin da kwayoyin halitun jini suka fara tarwatsewa acikin kokwan wato suka dauki wani salo na daban.

Me yasa ake kamuwa da ciwon dajin nono?

Wannnan dai kawai kowa ka iya kamuwa da ciwon, namiji ko mace mussaman mata masu shekaru da kuma masu gadonsa amma dai yanayin da rayiwa ta canza kowa ka iya kamuwa da cutar.

 

Karanta: 2019: Dalilan Da Ya Sa Bai Kamata ‘Yan Najeriya Su Sake Zaben Buhari Ba – Saraki

 

ALAMOMIN CIWON DAJIN NONO!!!
“””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””
1) Cangi yanayi girman nonon ki haka siddan
2) Jin wani sashin ajikin nonona naki ya zama kululu fiye da sauran sashin bangaren.
3) canjin yanayin fatar zuwa wani yanayi mara dalilin kamar kalar fatar lemon zaki.
4) canjin kalar fatar nonan yayi jaja wur ya kode zuwa kalar ja ta zagayen kululun kan nono nan (nipple) .
5) kankulun nonan (nipple) ya zama ya kumbura haka kawai kuma yana ciwo.
6) Fitar wani ruwa salkami haka kawai
7) Radadi da ciwo mai zafi akan nonan da kuma hammata ko da yaushe kuma haka kawai.
8.) Kumburin hammata tsakani allan kafata zuwa sashin nonan.

 

Karanta: Yadda Ake Amfani Da Albasa Wajen Maganin Kaushin Kafa [Hotuna]

 

Bugu da kari
””””””””””””'””””””

Ta ya ya mutum zai ake gane sanƙaran mama?

Abu na farko da za a fara lura a tabbatar da cewa jiki ya kamu da cutar sanƙaran mama shine samuwar wani dan tsiro a cikin nonon maras ciwo. Shi wannan tsiro za a ji shi kamar kurjin maruru sai dai ba ya ciwo. Duk macen da ta ji irin wannan a jikin mamanta sai ta garzaya wajen likitanta nan take.

Dole ne a cire duk ilahirin irin wannan tsiron sannan a gwada a asibiti. Maman da cutar sanƙara ta fara kamashi in an kalle shi a ido ba za a ga wani canji ba, haka kuma a jiki ma ba za a ji komai ba. Ba ya kawo ciwo, baya sa zazzabi, amai, gudawa ko rashin cin abinci kuma ba ya hana ayyukan yau da kullum. Ba lallai ba ne a ce kin taɓa ganin ko jin labarin cutar ba, domin mai yiwuwa ne a ce bata taɓa kama wani dan uwanki ba ko wanda kika sani. A wannan mataki na farkon shigar wannan cutar akwai fatan cewa in dai aka yi maganin wannan cutar za a iya warkar da ita.

Sanƙaran mama kuma tana iya farawa ta hanyar fitowar ciwo a kan mama ko fatar da ta zagaye kan maman.

A wasu matan kuma, kan nonon ne zai fara shigewa ciki. Za’a ga mazaunin sa ba daya yake dana ɗaya ɓangaran ba.

 

Karanta: Yadda Ake Amfani Da Albasa Wajen Maganin Ciwon Sanyi Da Mataccen Maniyyi

 

Idan kika ga kan nonanki ya lotsa ciki.
A nan cutar ta riga ta haɓaka don haka ya kamata a ce an zo asibiti tun kafin cutar ta kawo wannan matakin. Idan aka kyale tsiron, ci gaba zai yi tayi da girma. Zai iya girma daga cikin maman har ya ratso fatar maman ya zamo gyambo (ciwo) wanda yake fitar da ruwa da jinni mai wari, kuma ba zai warke ba sai anyi maganin wannan cuta.

A sa’ar da wannan cuta ta cigaba da bunƙasa, ta kan bazu zuwa wasu sassa na jiki kamar ƙwaƙwalwa, hunhu, kasussuwa da hanta ta wata hanya da ake kira (Metastasis) da turanci. Ita wannan bazuwar zuwa ga wadannan gabobin ne ke cutarwa, kuma da zarar hakan ta faru, duk da cewa bayar da magani ya zama dole, samun waraka abu ne mai wahala.

Za a iya gane irin wannan buzuwar cutar ta hanyar samuwar tari, haki, kumburin ciki, ciwo a kasussuwa musamman ma baya, rashin ƙarfin ƙafafu da rashin iya motsa su.

 

Karanta: Rikicin Shi’a: Kotu Ta Sake Dage Sauraren Shari’ar Malam Ibrahim El-Zakzaky

Sai dai kuma ciwo da kumburi nono na iya zama nasaba da wani abu daban saka makon.

Shin za a iya gane cutar sanƙaran mama da wuri?

Za’a iya gane wannan cuta da wuri ta hanyar lura da halin da maman ke ciki. Wannan wadansu matakai ne da mace zata riƙa bi sau daya a wata domin ta duba mamanta ko akwai wani tsiro, kumburi, ko wata cuta a jikin maman. Ya kamata ki buƙaci likitanki tkoya miki yadda zaki riƙa duba mamanki ita ma kuma ta duba miki mamanki a ƙalla sau daya a shekara. Daukan hoton mamman a asibiti don binciken cutar, na iya taimakwa wajen gano tad a wuri.

 

Karanta: Yadda Ake Gullisuwa

 

Matakan Sanƙaran Mama

Ana iya fahimtar tsanin bazuwar da wannan cuta tayi a jikin marar lafiya ta hanyar matakin da cutar take a wannan lokacin. Waɗannan matakai su ne:

Mataki na I: Tsiron cikin maman da bai kai sentimita biyu ba, ko kuma yana daidai da sentimita biyu. Kuma idan aka gwada kaluluwar hammata za’a ga babu wannan cuta.

Mataki na II: Faɗin tsiron cikin maman yana tsakanin sentimeta biyu zuwa biyar tare da kaluluwar hammata wacce ta nuna akawai cuta ko kuma wacce ta nuna babu cutar. Zai kuma iya kasancewa faɗin tsiron cikin maman ya wuce sentimeta biyar tare da kaluluwar hammata wacce ta nuna cewa akwai cutar.

Mataki na III: Wannan matakin an kasa shi zuwa gida biyu IIIA da IIIB.

 

Karanta: Yadda Ake Hada Man Karas Mai Kara Tsahon Gashi

 

IIIA: A nan faɗin tsiron cikin maman ya fi sentimita biyar, kuma akwai kaluluwar hammata masu motsi waɗanda suke dauke da wannan cuta. Ko kuma girman kumburin zai iya zama ko ma ya ya da kuma kaluluwar wacce kaluluwar hammata waɗanda suka maƙalewa juna kokuma suna maƙale da wata tsoka dake wannan gurbin.

IIIB: A nan faɗin tsiron cikin maman zai zama ko yaya amma ya bazu zuwa fata, bangon ƙirji, ko kaluluwa da suke can kasan nono kuma a can cikin ƙirji.

Mataki IV: A nan faɗin tsiron cikin maman ko ma ya girmansa yake anan ya bazu zuwa wurare masu nisa kamar ƙasussuwa, hunhu, ko kaluluwar jiki da suke nesa da mama.

 

Karanta: Taimako Ga Masu Fama Da Sanko

 

Mataki na I da na II su ne farkon kamuwa da wannan cuta amma mataki na III da IV cutar ta riga ta bunƙasa.

Yaya ake maganin cutar sanƙaran mama?

Ana maganin sanƙaran mama sabuwar kamu ta wadannan hanyoyi:

Surgery (Fiɗa): Wannan shine a cire maman gaba daya ko wani ɓangarensa ta hanyar fida. Amma yin wannan fiɗa ya danganta da abubuwa da dama wanda zaki tattauna da likitanki.

Chemotherapy – Shine yin amfani da magani domin a kashe kwayoyin da suka gina wannan cuta, wadda ta riga ta bazu zuwa wasu ɓangarori na jiki ko a ƙanƙantar da wannan kumburi na mama. Duk da dai waɗannan magunguna su na da illoli, amma akwai hanyoyin da likitoci sukan bi domin taimakawa mai wannan cuta wajen samun saukin waɗannan illoli.

Hormone Treatment – yin amfani da wannan sinadari na homon domin su hana ƙwayoyin wannan cuta girma. Za a iya yin wannan ta hanyar fiɗa, radiotherapy, ko shan da magunguna.

 

Karanta: Bidiyo: Yadda Ake Hada Kunun Aya Mai Dan Karen Dadi (Yana Kara Lafiya)

 

Radiotherapy – yin amfani da ƙwayoyi na wuta wajen kashe ƙwayoyin wannan cuta.

Akwai hanyoyi da dama da ake bi a warkar da wannan cuta, sai dai ya danganta da bazuwarta a jiki, zabin mai ɗauke da wannan cuta, kuɗin da za’a iya kashewa, da yadda za a iya daurewa bin ƙa’idojion shan magani, da kuma kayan aiki da ake da su.

Yin maganin wannan cuta ya kan ɗau lokaci mai tsaho kuma ana buƙatar yawan zuwa asibiti. Yana da tsada kuma yakan dau lokaci. Duk wadannan abubuwa ne da suka zama dole a tattauna su da likita.

Haka kuma yana da kyau mai ɗauke da cutar sanƙaran mama ta tattauna da ‘yan uwanta domin su gane yadda cutar take domin su ba ta goyon baya da ƙwarin gwiwa, kuma su taimaka wajen faɗakarwa game da lura da mama.

 

Karanta: Zargin Magudin Zaben 2019: Hukumar INEC Ta Maida Wa Obasanjo Martani

 

Sakamakon magani

Karbar magani ga jiki ya bambanta daga mutum zuwa mutum kuma ya danganta da:-

· Matakin cutar a lokacin da aka gano ta: Cutar da aka gano ta tunda wuri tafi saukin warkarwa.

· Yanayin cutar sanƙara: Sauƙin warkewar ya danganta da irin cutar sanƙarar da ta kama mutum. Ana gane irin cutar ne bayan an yi gwaje-gwaje akan tsiron da aka ciro daga jikin mai ɗauke da cutar.

· Bin Ƙa’idojin magani ba tare da kuskerawa ba.

Idan babu kumburi a hammata kuma girman sanƙaran bai wuce girman sentimita uku ba ko ƙasa da haka, kashi casa’in da tara cikin dari na waɗannan majinyatan sukan rayu har tsahon shekara biyar. Haka kuma kashi sittin cikin dari na majinyatan da suke da kaluluwar hammata guda biyu zuwa hudu za su iya rabuwa da cutar a cikin shekara biyar in aka haɗa da kashi arba’in cikin dari na masu ɗauke da kaluluwa shida zuwa goma.

 

Karanta: Gobara Ya Yi Sanadiyyar Asarar Dukiyoyi A Wata Babbar Kasuwa A Arewa

 

Idan kuma cutar ta riga ta bunƙasa fa? A na nufin kenan ba za ta warke ba? To in da rai da robo. Domin ƙididdigar da aka bayar a sama, ta samu ne ta hanyar hada sakamakon mutane da yawa da aka yi. Babu likitan da zai ce lallai yadda aka samu din nan, haka ne zai faru a kanki, koda a ce an yi ta maganin amma cutar ta ki warkewa, likita zai iya bakin ƙoƙarinsa wajen bada magunguna waɗanda za su rage zafin cutar.

To magungunan gargajiya fa? Abun sani anan shine, duk wanda yake jinyar mai ɗauke da cutar sanƙara, fatansa ne a samu sauƙi da wuri saboda mai cutar ta daina shan wahala. Abin takaici shine, cigaban da aka samu akan shawo kan cutar a kimiyyance bai taka kara ya karya ba. Amma duk da haka, yafi amfani nesa ba kusa ba, yafi rashin cutarwa, kuma yafi tabbaci fiye da kowane irin hanyar magani da wani ko wata zai zo miki dashi a yanzu. A ƙarshe, mutum zai iya taimakawaa ckin binciken samo maginin da yafu na yanzu aiki ta hanyar ba da gudunmawa da haɗin kai ga masu bincike a asibiti.

 

Karanta: Yadda Za Ka Fita Duk Wani Tsarin MTN Mai Cinye Ma Ka Katin Waya

 

Yana da mutuƙar amfani mutum ya zo asibiti da wuri da zarar ya lura da waɗansu canje-canje don neman magani.

Me yake jawo sanƙaran mama?

Mutane da dama sukan so su san abinda yake jawo wannan cuta ta sanƙaran mama. Har ma sukan tambayi kansu, me yasa na gamu da wannan cuta? Ko me ya sa matata ko ƙanwata ko ya ta ko ƙawata ta gamu da wannan cuta? Ko akwai wani abu da na yi ko suka yi, da ya kamata su yi, ko na yi, da banyi ba, ko basu yi ba domin kare kai na ko kansu daga wannan cuta?.

Babu wani sanannen dalili da za a iya kawowa kai tsaye wanda za a ce shi yake kawo wannan cuta. Sai dai akwai wasu dalilai da sukan sanya wannan cuta ta fi saurin kama wasu matan a maimakon wasu.

 

Karanta: Wani Magidanci Ya Kashe Uwargidansa, Da ‘Ya’yansa 2 Tare Da Wasu Mutane 4

 

Waɗannan dalilai su ne:

· Shekaru – Ƙarfin zaton kamuwar mace da sankaran mama, yana karuwa ne da yawan shekarun mace.

· Sinadarin iyistirogin – Yawan Sinadarin iyistirogin da yake jikin mace. Shi wannan sinadari na iyistirogin yana ɗaya daga cikin sinadaran da jikin mace ya ƙunsa kuma yana da kyau a ce jikin mace yana da wannan sinadari isashshe. Sai dai kuma bai kamata a ce jiki yana fitar da shi ba tare da hutu ba.

 

 

Wannan hutun yana zuwa ne a lokacin da mace take da ciki ko take shayarwa. Don haka dalilan da suke haifar da kasancewar sinadarin iyistirojin a jiki suna jefa jiki cikin haɗarin kamuwa da cutar sanƙaran mama. Daga ciki akwai fara jinin al’ada da wuri (kafin a kai shekara goma sha biyu), yin al’ada har a wuce shekara hamsin da biyar, rashin haihuwa, da kuma jinkirin haihuwa da wuri har a wuce shekara talatin.

 

Karanta: Yadda Ake Cika Fom Din Neman Aikin Sojojin Ruwan Nijeriya (Nigerian Navy) A Yanar Gizo

 

Waɗannan abubuwa ba yin kanmu ba ne, kuma za a iya saisaita yawan wannan sinadari a jiki ta hanyar shan magungunan hana ɗaukar ciki da na sa haihuwa da sauransu.

· Girman Jiki da sura- Mace mai tsaho da mace mai ƙiba ta fi faɗawa hadarin kamuwa da wannan cuta. Matan da sukayi ƙiba kuma basu rame ba har bayan sun daina jinin al’ada haɗarin kamuwarsu da sanƙaran mama yafi yawa. Haka kuma komai shekarun mace, wanda suke da tarin kitse a tumbin su ko kuma a ƙugun su suma hadarin kamuwarsu da sankaran mama yafi yawa

· Tarihin cuta a cikin ‘yan uwa – Macen da a cikin yan uwanta an taɓa samun wata kamar mahaifiyarta, ko yarta, ko ‘yarta ta tana da wannan cuta, ta fi fadawa haɗarin kamuwa da wannan cuta.

· Tarihin Kamuwa da cutar Sanƙaran mama: Macen da cutar sanƙara ta taɓa kama ta a mamanta guda ɗaya, cutar za ta iya kama ɗaya maman ma

 

Karanta: Tsaro: Rundunar F-SARS Ta Fita Daga Tarayya Ta Koma Jihohi

 

· Wasu cututtukan mama da ba sanƙara ba: Wasu matan da aka taɓa cire musu tsiro a mamansu wanda likita ya ce musu ba sanƙara bane. Dole sai suna zuwa a na duba wannan mama akai-akai domin irin wannan tsiro zai iya juyawa ya koma cutar sanƙara daga baya

Akwai tabbacin cewa kamuwa da cutar sanƙaran mama ba laifin mutum ba ne. Bata da alaƙa wacce take kai tsaye da abincin da muke ci, kuma ba cuta bace mai kwayoyi da za’a iya kamuwa dasu ba. Haka kuma ba a daukar ta ta hanyar jima’i, ko ta hanyar hulda da wanda yake da wannan cuta.

AL’ADA (PERIOD CYCLE)

Lokacin zuwan jinin al’ada wasu matan nononasu na nauyi, zafi, kumburi, radadi da sauransu amma bayan nan sai ya koma kalau bayan tafiyar jinin na al’ada.

 

Karanta: Amfanin Aya 7 Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

 

BAYAN KO KAFIN HAIHUWA

Nono kan canja yai samar da wani yanayi na daban Lamar:-

Radadin kan kululu
Karin girman nono
Canjin kalar kululu zuwa baki.
(Wasu matan kan samu wani yanayi sabanin wannan)

Leave A Reply

Your email address will not be published.