GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Allah Gwani: Abubuwan Mamaki Dangane Ga Kwaƙwalwa

Allah Gwani: Abubuwan Mamaki Dangane Ga Kwaƙwalwa

65

- Advertisement -

 

1] A yayin da ƙwayoyin hallitar ƙwaƙwalwa na wani ɓangare suka mutu, na wani ɓangaren suna iya ɗaukar aikinsu su cigaba. Misali, wannan ne yasa masu shanyewar ɓarin jiki suke warkewa.

 

Karanta: Da Duminta: Wasu ‘Yan Bata Gari Sun Lalata Akwatin Zabe Bayan Jami’an EFCC Sun Kama Wani Jakka Makil Da Kudin Na Sayan Kuri’un A Benuwe

 

2] Ƙwaƙwalwa ba ta ɗauke da maganaɗisan jin ciwo wato “Pain receptors”, saboda haka ba zata iya jin ciwo kamar yadda sauran sassan jiki kan ji ciwo ba. Saboda haka ciwo daga kai yana zuwa ne daga sauran abubuwan da ke kewaye da ƙwaƙwalwa.

 

3] Ƙwaƙwalwa ta fi kowanne sassan jiki son kanta. Domin duk da cewa nauyinta baya wuce kaso uku cikin ɗari (3%) na nauyin jikin mutum, amma dole sai an bata kaso talatin cikin ɗari (30%) na yawan jinin da zuciya ke harbawa a kowanne bugawar zuciya.

 

Karanta: Asiri: An Gano Sunan Gwamna El-rufai Kulle Cikin Likkafani A Makabarta (Hotuna)

 

4] A mafi yawan lokuta ɗan’adam yana amfani da dukkan ɓangarorin ƙwaƙwalwarsa , saɓanin tatsuniyar da ke cewa wai ɗan’adam yana iya amafani da ɗan wani sashi na ƙwaƙwalwarsa ne kawai.

 

5] Kimanin rabin sinadaren abincin da yara ke ci suna tafiya ne wajen gina ƙwaƙwalwa domin koyo.

 

Karanta: Uwar Jiki: Alaƙar Ciwon Gwiwa Da Kiba

 

6] Kamar yadda motsa jiki ko atisaye yake ƙara lafiyar jiki, haka ma yake ƙara lafiyar ƙwaƙwalwa.

 

7] Kamar yadda tambarin babban ɗan yatsan hannunka yake daban dana kowa, haka ma yadda ƙwaƙwalwarka ke aiki daban data kowa.

 

Karanta: Dalilan Da Yasa Muke Taka Rawa a Zabukan Nijeriya – Rundunar Soji

 

8] Saboda ƙwaƙwalwa tana aiki ne da tsarin lantarki, a yayin da mutum yake a farke, ƙwaƙwalwa na iya samar da ƙarfin lantarkin da zai iya kunna farin ƙwai.

 

9] Kimanin kaso sittin cikin ɗari (60%) na ƙwaƙwalwa kitse ne.

 

Karanta: Kadan Daga Cikin Ilolin Tsaka

 

10] Rashin isashshen bacci yana rage kaifin ƙwaƙwalwa. Dan’adam yana buƙatar baccin kimanin awanni bakwai zuwa tara a kullum.

 

11] Ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa basa iya jure rashin iskar oksijin da sinadarin gulukos na fiye da mintina biyar face sun mutu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.