GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Amfani Da Kuma Lahanin Cin Goro Ga Jikin Dan Adam

Amfani Da Kuma Lahanin Cin Goro Ga Jikin Dan Adam

28

- Advertisement -

Shi dai goro ‘ya’yan wata bishiyace dake da tarihi musamman a kasar Hausa wanda yakasance wani sashe na al’adar Malam Bahaushe da yake rabawa a tsakanin mutane a lokacin da wani albishir ya faru kamar na bikin aure,zanen suna ko halattar wani muhimmin taro.

 


Goro baya daga cikin jerin tsirran itatuwa kamar su lemu,kankana,ayaba ,abarba,gwanda,karas,goiba ,kwakwa wadanda ake cewa suna kumshe da muhimman sinadirran dake zama a matsayin magani ko sinadiran dake kara lafiya da gina jiki.

 

Karanta: An Gudanar Da Salla Raka’a Biyu A Gombe Domin Farin Cikin Nasarar Inuwa Yahaya

Goro ya kasance daban daga cikin jerin wadannan tsirran itatuwa.Idan aka tauna goro to zai bada abu biyu zai bada wasu ruwa masu barci,sannan ya bayarda tuka.wadannan ruwan suna daukeda sinadiran caffeine.ita kuma tukar tana daukeda sinadiran fibre.


Shi caffeine shi ne sinadirin dake sa a ji garau a lokacinda aka ci ko a sha wani abu dake dauke da shi.
Shi ne ake samu a cikin shayin Nescafe wanda yake aiki a cikin kwakwalwa domin samarda nishadi.

 

Karanta: An Kama Wani Mashayi Dan Shekaru 30 Mai Yunkurin Kashe Mahaifinsa


Shi kuma sinadirin fibre dake a cikin tukar yana taya hanji nika abinci ya kuma wanke hanjin wanda yana da amfani sosai ta wannan 6angaren.

Sinadirin caffeine da ake samu a cikin goro – yana warkarda ciwon kai (migraine).

Goro yana kara kaifin basira (cognitive booster) domin yana kara yawan iskan oxygen a cikin kwakwalwa.

 

Karanta: An Kama Wani Matashi A Garin Abuja Yana Satan Kamfen Mata

Goro na saurin narkarda abinci nan take domin sinadiran caffeine din suna kara yawaita samuwar acid dake a cikin ciki da kuma yawaitar enzyme wanda nan take yake narka abinci.

Goro na rage nauyin jiki sosai musamman ga masu kiba ko tai6a.

 

Karanta: A Baiwa Duk Wanda Ya Ci Zaɓen Gwamna A Kano – In Ji Abdulmumin Jibrin Kofa

Goro yana danne tashin zuciya -(nausea).Dan haka mai jin zuciyarsa na tashi a sanda yaci abinci sai ya nemi dan goro ya tamna.kada aci tamkar wanda ke cin abinci.cinsa da yawa kansa wani abu ya shiga.

Akoi wani abu da ake kira addiction(waton kamar mugun sabo da yin wani abu) ka sabawa jikinka da cin wani abu ko yin wani abu har ya kasance idan baka yi shi ba zaka ji wata damuwa.ko kuma wannan abin zai maka wahalar bari.misali shan sigari ko cin goron wanda idan aka saba dasu to a hakika suna da wahalar bari ko an bari sai kaga kwana biyu an dawo.

Illolinsa sun hada da yana kara yawaitar acid a cikin ciki wanda hakan wani lahanine musamman ga mai gyambon ciki domin zai kara ta’azzara zafin zuciya da kabrewar ciki. Dan haka mai fama da olsa sai ya nisanci tamna goro.

 

Karanta: Zaben Gwamnan Kano: Sanata Kwankwaso Ya Yi Kira A Zauna Lafiya

Yana sanya yawan fitsari domin shi extra caffeine baya azuwa a cikin jiki a dan haka hanta ce zata dauki nauyin sarrafa shi har ta fitarda shi ta hanyar fitsari  dan haka mai fama da matsalar yawan fitsari yana da kyau ya nisanci cin goro.

Yana kara hauhawan jini a sabili da karuwar bugun zuciya wanda caffeine din zai sanya nauyin aiki ga zujiya. Dan haka mai fama da hawan jin sai ya nisanci cin goro.

Yana sanya rashin bacci wanda daidai yake ga ka sha Nescafe dan hana idonka yin barci.Rashin bacci kuma yana haifarda tsangwama ga lafiyar jiki.Bacci hutune na musamman dake tafiyarda gajiya da samarda natsuwa da kwanciyar hankali.Rashinsa wata illace ta daban da zata iya janyo wasu matsaloli na daban.
Dan haka mai fama da karamcin bacci yana da kyau ya nisanci cin goro.

 

Karanta: Yankin Arewa Na Da Buƙatar Jagororin Irin Sanata Kwankwaso – In Ji Sheikh Ibrahim Khalil

Akoi bukatar tsofaffin da suka manyanta su nisanci cin goro wanda anan kasar Hausa zaka ga dan shekara 80 amma a kullum sai yaci kwallo uku na goro wanda wannan goron ba gina jiki yake yi ba asali zai fi amfani ace lemun zaki ne ake sha.Domin idan an manyanta karfin garkuwar jiki naja baya.kuma cutuka sun fi saurin afkawa tsofaffi dan suna da weak immune system.

Cin goro kan yiwa hakora lahani domin duk wanda ya shekara goma na cin goro to idan ka kalli hakoransa nan zaka ganewa idonka.

Mai fama da rashin lafiyar zuciya yayi kokari ya kauracewa cin goro.

Leave A Reply

Your email address will not be published.