GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Amfanin Ganyen Mangwaro 7 Ga Lafiyar ‘Dan Adam

Amfanin Ganyen Mangwaro 7 Ga Lafiyar 'Dan Adam

128

- Advertisement -

.

Ganyen Mangwaro wadanda ke da matukar amfani ga lafiyar dan Adam wajen kawar da cututtuka da dama.

A yayin da binciken masana kiwon lafiya ke ci gaba da bunkasa da kuma kari fadi ta fuskar zamani na kimiyya, ya tabbatar da cewa mafi akasarin magunguna da aka samar da su daga tsatso na itatu sun fi tasiri ga lafiya akan kowane nau’in magani da samo asali daga wasu sunadaran na daban.

Binciken da kwararru na bangaren kiwon lafiya suka gudanar ya tabbatar da cewa, baya ga amfani na ‘ya’yan itaciyar Mangwaro akwai kuma tarin arziki da ganyen itaciyar ya kunsa.

Karanta: Abubuwa Da Su Ka Sa Na Ke Goyon Bayan Atiku – Obasanjo

Ganyen Mangwaro ya kunshi sunadarai masu tasirin gaske ga lafiyar dan Adam wajen kawar da wasu cututtuka da suka saba addabar al’ummar musamman a wannan zamani. Ire-iren wannan sunadarai sun hadar da; tannins, anthocyanidins, beta-taraxerol, ethyl acetate da sauransu.

Da sanadin shafin jaridar Guardian, a yau kalace-kalacen mu ya bankado wasu muhimman tasirai gami da arzikin da Mai Duka ya sanya cikin Ganyen Mangwaro wadanda ke da matukar amfani ga lafiyar dan Adam wajen kawar da cututtuka da dama.

Karanta: Maganin Kowane Irin Basir

A yayin da binciken masana kiwon lafiya ke ci gaba da bunkasa da kuma kari fadi ta fuskar zamani na kimiyya, ya tabbatar da cewa mafi akasarin magunguna da aka samar da su daga tsatso na itatu sun fi tasiri ga lafiya akan kowane nau’in magani da samo asali daga wasu sunadaran na daban.

Binciken da kwararru na bangaren kiwon lafiya suka gudanar ya tabbatar da cewa, baya ga amfani na ‘ya’yan itaciyar Mangwaro akwai kuma tarin arziki da ganyen itaciyar ya kunsa.

Karanta: Yadda ake miyar kuka

Ganyen Mangwaro ya kunshi sunadarai masu tasirin gaske ga lafiyar dan Adam wajen kawar da wasu cututtuka da suka saba addabar al’ummar musamman a wannan zamani. Ire-iren wannan sunadarai sun hadar da; tannins, anthocyanidins, beta-taraxerol, ethyl acetate da sauransu.

A sakamakon wannan arziki na sunadarai da ganyen mangwaro ya kunsa da kuma tasiran su ga lafiyar dan Adam, Legit.ng ta kawo maku jerin wasu cututtuka da idan anyi amfani da Ganyen na Mangwaro akan samu waraka da izinin Mabuwayi.

Karanta: Amfanin Citta Ginger) Ga Lafiya Jikin Dan Adam

1. Ciwon Suga

Ana amfani da busasshen ganyen mangwaro da aka nike shi ya zama gari wajen magance cutar suga tun a matakinta na farko sakamakon tasirin sunadaran anthcyanidins da kuma beta-taraxerol da ya kunsa.

Kazalika ana kuma jika ganyen magwaro cikin ruwa na kwana guda kana a kwankwadi wannan ruwa domin magance cutar ta suga tun kafin ta ci karfin lafiyar dan Adam.

2. Cutar Hawan Jini

Ganyen Mangwaro ya na da matukar tasiri wajen saukaka cutar hawan jini ta hanyar inganta kuzari na tashoshi da shiyoyi masu aika sakonni na jini.

3. Kasala da rashin karfin jiki

Akan dumama ruwan wanka tare da ganyen mangwaro domin aikata hakan yana kawar da kasala tare da kara kuzari ga dan Adam.

Karanta: Illar Yawan Amfani Da Magungunan Jima’i (Shawara Ga Maza)

4. Tsakuwar ‘Koda

Ana amfani da gari na ganyen mangwaro wajen kawar ta wannan cuta sakamakon narkar da tsakuwar koda tare da tsarkake ta daga cututtuka.

5. Cututtukan tashoshin numfashi

Amfani da markadadde ganyen mangwaro tare da ruwan Zuma yana kawar da duk wata cuta da ta shafi tashoshin numfashi irin su Mura, Tari, Asma, disashewar murya da sauransu.

Karanta:

6. Cutar Atini

Akan kwankwadi Garin Ganye Mangwaro da aka jika da ruwa wajen samun waraka daga cutar atini ko da kuwa mai zuwa ce da fitar jini.

7. Ciwon Kunne

Akan dumama ruwan da aka tatso daga jikin Ganyen Mangwaro wajen digawa a cikin kunne domin kawar da radadi da cututtuka da suka shafi cikin kunnen dan Adam.

Leave A Reply

Your email address will not be published.