GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Amfanin Kanumfari a jikin Dan Adam

Amfanin kanumfari a jikin Dan Adam

72

- Advertisement -

AMFANIN KANUMFARI A JIKIN DAN ADAM
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Kanumfari nada Amfani ga lafiyar dan Adam domin yana Maganin Fungal, Bacteria da Virus wato cututukkan da bama iya ganin su kai tsaye ba tare da an saka madibin Likita ba (micro scpt).

A kasashe da dama ana amfani da kanumfari, kamar su Indunisia, America, India da Sauran.

kasashen turai, Yankin Africa ma ba’a bar mu a baya ba domin kusan ma duk mun fi sauran kasashe amfani da Kanumfari in ka debe India domin gaba daya kasar India ba inda ba’a amfani da Kanumfari Musamman ma bangaren yankin Arewa na India.

America Sukanyi amfani da kanumfari wajen girki da kuma saka shi a Buredi.

A kasar Netherland (holand) sukanyi amfani da shi wajen hada wainar Fulawa (cheese).

A kasashen Chana da Japan sukan yi sabulun da Kanumfari domin magance cutukkan da ke addabar fata.

YADDA ZA’A YI AMFANI DA KANUMFARI WAJEN NEMAN LAFIYA.

1.CIWON KAI
**************
(A), Yana maganin ciwon kai. A shafa
man kanimfari a goshi, Yana taimakawa wajen ciwon kai wanda ke faruwa sanadiyar mura.

(B), Idan kuma ciwon kan bana Mura bane, za’a iya samun Kanumfari guda biyar a saka a cikin ruwa kofi guda, a saka a wuta su tafasa sosai sai a saka Suger kamar Rabin cokali a ciki idan ya dan huce sai a sha ayi haka sau 2 a yini In shaa Allahu kan zai daina ciwo koda kuwa baya jin Magani ne.

2. CIWON HAKORI.
*******************
Yana maganin ciwon hakori. Zaka
iya amfani da man-kanimfari (clove oil)
ga hakori mai-ciwo ko kuma kanimfarin (dakakke) , a jikashi kadan da ruwa a lika wajen hakori mai-ciwo.
Idan mai ( clove oil) kake amfani dashi sai asamu auduga a zuba man kadan a lika wajen hakori mai-ciwo (ka danne da hakora).

3.WARIN BAKI.
***************
Za’a iya amfani dashi a matsayin
abun wanke baki. Yana maganin warin baki (a tafashi a yawaita wanke baki dashi sau 3 a rana).

4.MAGANIN AMAI
*****************
(A), Domin Tsayawar amai ga Mata masu ciki, a daka kanunfari biyu a sa babban cokali daya na zuma a sha yana maganin Amai ga macce mai ciki.
(B),Don magance amai baga mai juna biyu ba kuwa, a saka kanumfari 4 a cikin ruwa kofi daya a tafasa idan ya tafasa a saka sugar cokali daya a sha.

5.TYPHOID
***********
A samu ruwa littr biyu sai a saka kanumfari kamar guda 5 a cikin ruwan a tafasa ruwan kada a sauke sai ruwan sun koma sauran littr daya sai a sauke idan ruwan ya huce sai a riqa sha Wannan yana Maganin typhoid.

6. Ciwon Kunne;
****************
A hada Man kanun fari da Man Ridi a diga a kunne mai ciwo duk lokacin da za’a kwanta wannan yana maganin ciwon kunne.

7.MAGANIN MURA
*******************
Ga masu yin mura A tafasashi da citta/jinja (ginger) a sha shayi.

8. MAGANCE MAKERO/KYANDA
*****************************
Ana goga Man kanumfari a wurin da matsalar take wannan yana maganin Makero.

9. GIRMAN MAZAKUTA
***********************
Asamu nikakken kanumfari ko adakasa sai ajikasa da mansa ahada da man zaitun, sai ajika “gaba” dashi,idan za’a kwanta,da rana kuwa duk bayan anyi
wanka sai ashafa, wannan yana sa girman Azzakari.

10. KARFIN MAZAKUTA
************************
A samu Man kanumfari duk za’a yi saduwar aure awa daya kafin a fara a shafe gaba da shi.

11. KURAJEN HARSHE
**********************
Don Magance Kurajen Harshe, daka Kanumfari a saka a harshen a barshi zawon wani lokaci, ko kuma idan za’a kwanta a saka in shaa Allahu kafin safe zasuyi dama.

GODIYA GA ALLAH DA YA SAUKAR MANA ABUBUWA NA YAU DA KULLUM.

Leave A Reply

Your email address will not be published.