GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

An Ƙaddamar Da Sabon Sansanin Soja A Birnin Gwari

An Ƙaddamar Da Sabon Sansanin Soja A Birnin Gwari

18

- Advertisement -

Rundunar sojojin saman ƙasar nan ta ƙaddamar da wani Sabon sansani a ƙaramar hukumar Birnin Gwari, tare da tura jiragen yaki a yankin domin sake sabon damarar ci gaba da tunkarar ta’addancin ‘yan bindiga dadi.

 

Karanta: RIKICIN SARAUTA: Dan Majalisa Ya Maka Masarautar Gwandu A Kotu

 

Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar sojojin saman ƙasar nan Air Marshall Sadique Baba Abubakar ya ce, sun kuma tura jiragen yakin nan da ƙasar nan ta sayo daga kasar Italiya domin wannan aiki.

 

Babban Hafsan sojojin saman ya ce, sun kuma tura karin bataliyar mayakan sama na musamman wato “special forces ” da za su yi aiki daga kasa, duk dai a kokarin cimma yan ta’addan.

 

Sadique Abubakar ya ce sojojin saman ƙasar nan za su yi ta yakar ‘yan bindigar har sai sun tabbatar da tsaro a yankin na Birnin Gwari da ma sauran shiyyar Arewa Maso Yamma.

 

Karanta: Na Kammala Tsara Kunshin Mutanen Da Za Su Kasance Ministocina – Buhari

 

A cewar mai sharhi kan sha’anin tsaro Mohammed I. Usman, irin wannan hobbasar lalle ka iya ‘yin tasiri sosai wajen kawo karshen ‘yan bindigar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.