GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

An Gano Gawar Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Abaji

An Gano Gawar Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Abaji

42

- Advertisement -

 

An gano gawar mataimakin shugaban karamar hukumar Abaji, Mohammed Rizoma, kwanaki 10 bayan da ‘yan bindiga suka sace shi. An birne shi a kauyensa, Adagaba.

 

Daya daga cikin iyalan mamacin, Isyaka Mohammed, ya sanarwar manema labarai da wannan ci gaban, inda ya ce ‘yan sanda suka gano gawar na shi a dajij Gwajipa-Izom da ke jihar Neja a misalin karfe 1:45 na yamma.

 

 

Karanta wannan: Wani Matashi Bashir Ya Kashe ‘Yar Shekaru 3 Ta Hanyar Fyade A Zaria

 

Mohammed ya ce an gano gawar ne a yayin da har ya faru ruba, shugaban tawagar binciken inda gawar mataimakin ya ke ya kira shugaban karamar hukumar, Alhaji Abdulrahman Ajiya, wanda shine ya kira iyalan marigayin ya fada masu cewa an gano gawar mamamcin.

 

“A nan take ba tare da bata lokaci ba shugaban karamar hukumar ya bada umurnin aika motar asibiti dun daukar gawar” ya ce.

 

Karanta wannan: An Cafke Wata Ma’aikaciyar Jinya Tare Da Wani Malami Addini Masu Siyar Da Mahaifa Don Asiri

 

Ona Abaji, Alhaji Adamu Baba Yunusa, shi ya wakilci Ohimozi na Abaji, Yunusa Baba, a wurin binne mamacin sannan kuma ya roki Allah ya rahamshe shi.

 

“Ina mai rokan Allah ya tona asirin wadanda suka aikata wannan mummunar aiki,” ya ce.

 

Karanta wannan: Tsoho Dan Shekaru 78 Ya Furta Kisan Mata 90 (Hotuna)

 

Marigayi mataimakin shugaban karamar hukumar tare da dansa da direbansa a ranar Litinin da daddare na makon da ya gabata ‘yan bindiga suka sace  su a hanyar Lambata-Izon kusa da Suleja a jihar Neja.

 

Iyalan mamacin sun biya kudin fansar naira miliyan N3 ga ‘yan bindiga amma sai da suka kashe shi sannan suka sako direbansa tare da dansa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.