GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

An Sace Mutane Sama Da 30 A Kwanaki Biyu Kacal A Hanyar Kaduna-Abuja

An Sace Mutane Sama Da 30 A Kwanaki Biyu Kacal A Hanyar Kaduna-Abuja

19

- Advertisement -

A yayin da garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a Nijeriya, al’ummar arewacin Nijeriya na ganin babu wani abu da ya zama musiba ga jama’a yankin a wannan lokacin kamar satar mutane.

Karanta: ‘Yan Bindiga Sun Sace Wasu Masu Sayarda Itace a Kaduna

Rahotanni sun bayyana cewar cikin ‘yan kwanaki biyu da suka gabata an sace mutane sama da 30 a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Yawancin mutane na ganin hakan nada nasaba da yadda mahukunta ke nuna halin ko in kula akan wannan lamarin, wata mata dake bayyana ra’ayinta da cewar, ai don ba’a gabatar da wani hukunci mai tsanani ne yasa matsalar ke kara ta’azzara.

A bangare daya kuwa Kaftin Garba Shehu mai ritaya, yana ganin cewar rashin samar da isassun kayan aiki, da jami’an tsaro a wadannan yankunan ke kara sa abun yana daukar wani salo.

Karanta: Kotu Ta Yankewa Wasu Matasa 4 Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Laifin Sata

Don haka akwai bukatar mahukunta su tashi tsaye wajen samar da matakai da suka dace, don kawo karshen wannan matsalar da ta saka jama’a cikin halin ha’ulail.

Leave A Reply

Your email address will not be published.