GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

An Samu Hatsaniya Tsakanin Masu Zanga-zanga Da ‘Yan Sanda A Katsina

An Samu Hatsaniya Tsakanin Masu Zanga-zanga Da 'Yan Sanda A Katsina

21

- Advertisement -

 

Arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro tayi sanadiyyar asarar rai ‘daya da jikkata wasu da dama a jihar Katsina

 

Karanta: Shugaba Buhari Ya Rusa Dokar Rike Bindiga

 

A yammacin jiya ne zanga-zanga ta barke a karamar hukumar Batsari bayan kawo gawawwakin Mutane 13 da Yan bindiga suka kashe a kauyen Yargamji dake a karamar hukumar ta Batsari.

Jami’an tsaro sunyi amfani da karfin da ya wuce kima wajen dakile zanga-zangar Wanda har yakai ga sanadiyyar asarar rai da Kuma jikkata wasu da dama.

Karamar hukumar Batsari tana fuskantar matsalar tsaro Wanda yan ta’adda ke cin karensu ba babbaka, mazauna yankin sun koka game da rawar da jami’an ‘yan sandan ke takawa a yankin.

 

Karanta: Abinci 5 Da Ke Kara Ingancin Barci

 

Allah ya kawo Mana karshen wannan musibar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.