GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

An Tsinci Gawar Tsohuwar Budurwar Mawaki Diddy Mace A Dakinta

An Tsinci Gawar Tsohuwar Budurwar Mawaki Diddy Mace A Dakinta

29

- Advertisement -

An tsinci gawar tsohuwar budurwar shahararren mawakin kasar Amirka, P. Diddy, mace a cikin dakinta.

Tsohuwar budurwar mawakin, Kim Porter, ita ce mahaifiyar ‘ya’yar mawakin 3.

Ta rasu da shekaru 47 a Duniya.

Karanta wannan: Sh’i: Dalilin Da Ya Sa Ba Zamu Saku El-Zakzaky Ba -Gwamna El-Rufa’i

 

A cewar mujallar TMZ, an tsinci gawar tsohuwar budurwar shahararren mawakin wanda suka yi soyayya na tsawon shekaru 13 a gidanta da ke birnin Los Angeles a ranar Alhamis.

An samu labarin cewa an jami’an tsaro na yankin sun samu kiran neman agaji daga hukumar gidajen Porter’s Toluca Lake home da yamma a kan cewa akwai wata mai bukata likitoci su duba ta.

Karanta wannan: An Cafke Matasan Da Suka Shahara A Sace Matan Aure Tare Da Yi Masu Fyade A Kano (Hoto)

Duk da cewa ba’a tabbatar da abunda ya janyo mutuwar na ta ba tukun wani mijiya daga mujallar TMZ ta bayyana cewa Kim tana fama da mura wanda ake ganin cewa pneumonia ne na tsawon makonni.

Wani mai wakilin mawaki Diffy ya tabbarwa mujallar TMZ da faruwar hakan, inda ya ce “Ina bakin cikin tabbatar ma ku da rasuwar Kim Porter. Ina son ku baiwa iyalanta wani dan lokaci don su yi jimamin rashin da suka yi.”

Karanta wannan: Jami’an NSCDC Ta Cafke Wasu Masu Garkuwa Da Mutane A Neja

Kim tare da Diddy suna da ‘ya’ya 3 tare, sun samu ‘yan biyu James da D’Lila, ‘yan shekaru 12 da kuma Christian Combs dan shekaru 20.

Leave A Reply

Your email address will not be published.