GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

An Yi Aure Babu Amarya Saboda Ango Ya Kasa Samun Mata

An Yi Aure Babu Amarya Saboda Ango Ya Kasa Samun Mata

34

- Advertisement -

Wani matashi dan kasar Indiya mai suna Ajay Barot mai shekaru 27 a duniya ya angwance, amma fa ba tare da amarya ba, bayan da iyayensa suka daura masa aure shi kadai.

 

Karanta:: ‘Yan Bindiga Sun Wargaza Garuruwa Sama Da 98 A Jihar Zamfara

 

Ajay dai ya gaza samun mata ne a sakamakon ‘yar matsalar kwakwalwa da ya ke da shi da ke hana sa koyan abu da wuri.

Yin aure dai na daga cikin manyan burikan Ajay a rayuwa, a don haka ne ma iyayensa suka yanke hukuncin cika masa wannan buri ko da mata ko ba mata.

Ajay wanda dan jahar Gujarat ne dake kasar Inidya ya samu irin bikin da ya ke so dauke da kade-kade, baki, abinci da al’ada.

 

Karanta: Maganin Harbin Kunama

 

Kimanin mutane 200 ne suka halarci shagulgulan bikin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.