GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

ASUU ta yi Allah Wadai da yunkurin Aisha Buhari na kafa jami’a mai zaman kanta

ASUU ta yi Allah Wadai da yunkurin Aisha Buhari na kafa jami’a mai zaman kanta

16

- Advertisement -

Kungiyar malaman jami’a ta kasa, ASUU, a yau Talata ta caccaki gwamnatin tarayya bisa goyon bayan kafa jami’a mai zaman kanta da mai dakin shugaban kasa ta ke shirin yi, wanda ta bayyana cewa za ta sanyawa jami’ar sunan mijinta, Jami’ar Muhammadu Buhari.

 

Karanta: Everywoman: Mata Don Allah A Koyi Iya Yin Girki

 

ASUU ta zargi gwamnati da cewar wannan yunkuri na mai dakin shugaban kasa ya nuna a bayyane dalilin da ya sa Buhari ya ci gaba da rage kasafin kudin da ake warewa bangaren ilimi shekara bayan shekara tun bayan da ya karbi ragamar mulkin Nijeriya a shekarar 2015.

 

Shugaban kungiyar ASUU reshen jami’ar Ibadan, Farfesa Deji Omole da kuma ma’ajin kungiyar na kasa, Farfesa Ademola Aremu ne suka bayyana hakan a hira daban-daban da suka gudanar da manema labarai a birnin Ibadan.

 

Karanta: Maganin Radadi Da Zafin Ciwon Hakori

 

In ba a manta ba dai, mai dakin shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, a wajen wani taro a garin Yola,  ta bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa na kafa wata jami’ar kudi da za ta sanyawa sunan mijinta.

 

“A lokacin da na samu labarin cewa wai mai dakin shugaban kasa za ta kafa jami’a mai zaman kanta kuma za ta sanyawa jami’ar sunan shugaba Muhammadu Buhari, sai na ce wannan ba komai bane face rainin hankali. Ya za a yi a ce shugaban kasar da ya gaza wajen bawa ilimi kasafin da ya dace, kawai wai sai a ji iyalinsa da hadin gwiwar wasu ‘yan kasar waje, za su kafa jami’ar kudi a cikin Nijeriya. Wannan ko shakka babu hau ne ga kasar Nijeriya, haka kuma ga shugaban kasa mai ci,” a cewar Farfesa Omole.

 

Karanta: Cututtukan Da Tafasasshen Ruwan Albasa Ke Magancewa

 

Ya ci gaba da cewa, “Wannan ya tabbatarwa da ‘yan Nijeriya cewa Shugaba Buhari ba shi da niyyar inganta makarantun gwamnati.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.