GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Atiku Dan Asalin Kasar Najeriya Ne Kuma Jikanmu Ne – Wani Basaraken jihar Jigawa

Atiku Dan Asalin Kasar Najeriya Ne Kuma Jikanmu Ne – Wani Basaraken jihar Jigawa

25

- Advertisement -

Wani basarake a masarautar Dutse, jihar Jigawa, ya tabbatar da cewa mahaifiyar dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ‘yar asalin jihar Jigawa ce daga masarautar Dutse.

 

Karanta: Everywoman: Irin Abincin Da Ya Kamata Mace Ta Ci Bayan Ta Gama Haila

 

Basaraken dai ya ki amincewa da a bayyana sunansa sakamakon siyasantar da asalin Atiku da aka yi, amma ya tabbatar da cewa mahaifiyar Atiku Abubakar ‘ya ce ga Abdullahi, mutumin Jigawar Sarki, karamar hukumar Dutse, jihar Jigawa.

 

Basaraken ya yi wannan bayanin don ya jaddada gaskiyar Atiku Abubakar da ya bayyana cewa mahaifiyarsa ‘yar asalin jihar Jigawa ce bayan da jam’iyyar APC ta kalubalanci asalinsa na kasancewa cikakken dan Nijeriya a matsayin martanin kan karar da Atikun ya shigar kan sahihancin sakamakon da ya bawa Shugaba Buhari nasara a babban zaben da ya gabata.

 

Karanta: Everywoman: Mata Don Allah A Koyi Iya Yin Girki

 

“A matsayina na uban kasa a nan jihar Jigawa, bana so a ambaci sunana a matsayin wanda zai bada shaidar tabbacin Atiku Abubakar a matsayin dan asalin Nijeriya wanda ke da alaka da jihar Jigawa ta bangaren uwa ba, saboda yanayi na siyasa da zargin ke da shi.

 

“Amma ina mai tabbatar da cewa Marigayiya Kande ‘yar asalin garin Dutse ce kuma kawunta, Adamu Ma’aruf, ya kasance shi ne limamin babban masallacin Dutse har zuwa 1996 lokacin da ya rasu.” inji Basaraken.

 

Shi ma wani dattijo mai kimanin shekaru 100 a duniya, Isyaku Adamu, ya tabbatar da wannan batu, inda ya kara da cewa, ” Kande ‘Yar Malam ta auri Garba, wanda asalinsa mutumin Sokoto ne, kuma Garba shi ne mahaifin Atiku.

 

Karanta: Direba Make Da Ruwan Giya Ya Murkushe Yara 6 Har Lahira A Gombe

 

“Kafin ya auri Kande, Garba ya zauna a gidanmu da a ke kira da gidan Malamai, inda a nan ne ya hadu da mahaifiyar Atiku, ya aureta kuma ya dauke ya tafi da ita Adamawa, inda a can ne aka haifi Atiku.

 

“Mahaifiyar Atiku wato Kande kanwa ce ga Alhaji Ali da Azumi wadanda sun dade da rasuwa. Kande ‘yarmu ce, shi kuma Atiku jikanmu ne. Mu Fulani ne kuma kakanninmu malamai ne shi yasa ma ake kiran gidanmu da gida Malamai.” inji dattijo.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.