GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Ayyukar Ibadah Da Ake So A Yawaita Yin Su A Ramadan

Ayyukar Ibadah Da Ake So A Yawaita Yin Su A Ramadan

44

- Advertisement -

Abubuwan Da Ake So A Yawaita Su A Ramadan

1-Yawaita karatun Alkur’an,da tafsirnsa da kokarin sanin ma’anoninsa

2-Yawaita kyauta, musamman ga ‘yan uwa da abokai da masu karamin karfi

3-Sadaka da ciyar da mai azumi lokacin bude baki da lokacin sahur

4-Yin sallar nafila na rana dana dare.(Tarawihi ko Tahajjudi)

 

Karanta: Na Kammala Tsara Kunshin Mutanen Da Za Su Kasance Ministocina – Buhari

 

5-Shiga i’tikafi da yawaita ibada ta musamman

6-Yawaita yi wa Annabi salati

7-Yawaita neman gafara (Istigifari) da tuba da komawa zuwa ga Allah

8-Zuwa wajen wa’azi da sauran darussa kamar tafsir da sauransu

9-Yawaita yin tuba ga Allah da mayar da hakkin ga masu shi da nisantar sabon Allah

10-Ciyar da abinci dafaffe da danye

11-Kiyaye salloli akan lokaci da taimakon mahaifa

 

Karanta: Mayakan Boko Haram Sun Kwashi Kashinsu A Hannu A Wata Gwabzawa Da Suka Yi Da Sojoji

 

Sheikh Muhammad Salih al-Munajid ya fada a cikin littafinsa (As-siyam) cewa: “Daga cikin abubuwan da ke wargaza kyawawan ayukkan mutum kuma su haifar masa da zunubai musamman a lokacin azumi,akwai kallon finafinai,da wasanni, da sharholiya,da zuwa wajen taro mara anfani,da zama a kan kwalbati ko kan hanyar jama’a, da yawo a mota ko mashin a cikin gari ba tare da dalilin da shari’a ta yarda da ya gajiyar da kansa da rana ba, yadda da daddare ya kasa yin karatun al’qur’ani ko sallar tahajjud

Don haka ba a yarda mai azumi ya rinka ;

1-kallon fim din ‘yan Hausa, fitsararru masu yada fasadi da vata tarbiyya,da duk wani fim na batsa ko wanda ya ke nuna rashin kunya ko rashin kirki.

 

Karanta: Ramadan: Irin Kalar Abincin Da Ake So Mai Azumi Ya Rika Ci

 

2-Zuwa kallon qwallo:Bai halarsta ga mai azumi ya je ya kalle su ba, domin kallon qwallo haramun ne,akwai nuna tsiraici kamar fitar da cinya wanda bai halasta ba ga namiji da mace. Manzon Allah ya ce cinya tana daga al’aura. Haka ya gaya wa wani mutumi da ya fitar da cinyarsa. Sai ya ce masa, ‘Rufe cinyarka domin cinya tana da ga ala’ura
[61]

3-Karta da caca Allah ya hana su a cikin suratul Ma’ida su ma haramun ne ga mai azumi da ma wanda ba ya azumi

4-Hira da ‘yammata

Ya Allah ka isar da rayuwar mu ga wannan wata muna imani da kyakkyawar niyya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.