GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Ba za ki iya rike shari’an Atiku ba, mijinki sanatan APC ne – PDP ga Bulkachuwa

Ba za ki iya rike shari’an Atiku ba, mijinki sanatan APC ne – PDP ga Bulkachuwa

32

- Advertisement -

 

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sanya zargi akan karar da tsoon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya shigar game da zaben Shugaban kasa.

 

Karanta: Yadda Ake Gullisuwa

 

PDP ta bayyana cewa alkalin da ke rike da shari’an Atiku, Zainab Bulkachuwa, ta kotun daukaka kara ta kasance mata ga zababben sanatan jam’iyyar All Progressives Congress (APC)

Jam’iyyar adawan ta nemi Zainab ta janye daga matsayinta na Shugabar kotun da ke zama kan lamarin, tare da tsoron cewa tana iya yin son kai a shari’anta

A tsoron cewa Justis Bulkachuwa za ta yi son kai a hukuncinta, jam’iyyar PDP a wata wasika ta nemi ta sauka daga matsayinta a kotun.

Jam’iyyar adawar, a wata wasika dauke das a hannun shugabanta da sakatarenta, Prince Uche Secondus da Sanata Umar Tsauri, ta jadadda cewa babu tabbacin kasancewa a tsakiya a bangaren alkalin.

A halin da ake ciki, ta rahoto a baya cewa Atiku Abubakar dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, zai amince da hukuncin kotun zabe game da karar da ya shigar, hadimins,Segun Showunmi ya bayyana.

Ya kara da cewa, sai dai akwai alamu da ke nuna cewa Atiku zai samu yancinsa.

 

Karanta: An Yi Aure Babu Amarya Saboda Ango Ya Kasa Samun Mata

 

Karar da yashigar na kalubalantar sanar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zabe wada hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tayi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.