GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Baba Buhari Yawon Ya Isa Haka Na – Rokon Rahma Abdulmajid

Baba Buhari Yawon Ya Isa Haka Na - Rokon Rahma Abdulmajid

20

- Advertisement -

1 wani bincike da jaridar Punch ta taba yi ya nuna cewa a shekarar farko ta mulkin Baba Buhari ya karade kasashen duniya 30, tun ana shimfida masa tabarmar maraba ana fareti ana karbarsa da marmari har sai da ya koma shiga garuruwan ko ciyaman lokal gamman ba a turowa. Ko matukin jirgin sama in ya je kasa talatin a shekara ana kara masa tauraruwa daya a kafada.

 

Karanta: Babban Burina Shi Ne Ganin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso Ya Wulakanta A Siyasance – In Ji Magaji Overoll.

 

2 Wata majiyar kuwa zana katuwar taswirar kwallon duniya tayi Inda aka daddangwari kan kasashen da Baba ya je a shekara daya da tawada.

3 A yau kuma jita jita na karade wa cewa an gayyaci Baba kasar Faransa kuma ya amsa zai tafi.

4 Abu mafi girgiza zuciya shine Baba zai bar Najeriya awoyi kadan bayan an rantsar da shi a 29May dinnan. Kuma kun san Inda za shi? Saudiya zai kowa. Kenan a wata daya zai shiga kasa daya sau 2!

 

Karanta: Kisan Zamfara: Zamfarawa Ba Sa Kwana A Gidajen Su Yanzu- Marafa

 

Don Allah Baba na tuba. Ni ba ma tsiwa nake ba, roko nake ka zauna mu ma Mu dana ko….bari dai ba sai na ce ba saboda azumi. Ga map din yawon dai a duba, dama cewa zan yi na ga saura kadan ka ziyarci ruwa Baba. Kada yajuju da majuju su gayyace ka bangon duniya a nemeka a rasa Baba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.