GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Bai Kamata A Daura Alhakin Raguwar Kudin Dangote A Kan Manufofin Gwamnatin Buhari – Inji Taurarin Kannywood

Bai Kamata A Daura Alhakin Raguwar Kudin Dangote A Kan Manufofin Gwamnatin Buhari - Inji Taurarin Kannywood

16

- Advertisement -

Taurarin fina-finan Kannywood sun yi tsokaci kan masu sharhin da suka dora alhakin raguwar kudin Alhaji Aliko Dangote a kan manufofin gwamnatin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

 

Mujallar Forbes ta wannan shekarar ta wallafa cewa har yanzu sunan Dangote ne a farko a jerin masu kudin Afirika da dala biliyan 10.3.

 

 

Karanta: Da Duminta: Sama Da Sojoji 600 Sun Bata A Jahar Yobe

 

Wannan na nuna cewa arzikinsa ya ragu da kusan dala biliyan biyu, a cewar mujallar.

Mujallar Forbes din ta nuna cewa matsalar kasuwa ce da kamfanin siminti na Dangote ya fuskanta ya jawo raguwar kudin.

A nasa bangaren, Mike Adenuga, shugaban kamfanin sadarwa na Globacom, shi ne yazo na biyu a jerin sunayen masu kudin da kusan dala biliyan 9.2.

 

Karanta: 2019: Ba Mu Amince Da Goyon Bayan Buhari Ba – Kungiyar Fulani Ta Gan Allah

 

A bara dai jumallar ta ce arzikin Mike din dala biliyan 5.3 ne, wanda haka ke nufi arzikinsa ya karu.

Taurarin na Kannywood na ganin bai kamata a dora alhakin raguwar arzikin Dangote kan gwamnatin Shugaba Buhari ba, sannan a yi gum da baki kan karuwar arzikin Adenuga ba tare da an yaba wa gwamnatin ba.

Ce-ce-ku-ce kan batun

Daya daga cikin daraktocin Kannywood, Aminu Saira ne ya soma da tambayar BBC Hausa: ‘Shi kuma Mike Adenugu da arzikinsa ya karu wa aka dora wa alhaki?

Daga nan ne jarumi Saddiq Sani Saddiq ya nuna cewa tambayar da Aminu Saira ya yi ta burge shi, inda cikin arashi ya kara da cewa “watakila shi mike Adenuga dan Ghana ne”.

 

Karanta: 2019: Lamido Ya Caccaki Shugabannin Izala A Kan Goyon Bayan Buhari

 

Sai dai shi ma darakta Nasir Gwangwazo ya mayar wa da Aminu Saira raddi, yana mai cewa “ai ba BBC Hausa ne suka fada ba; masu sharhi ne. Don haka ina ganin ba BBC Hausa za a yi wannan tambayar ba”.

 

Karanta: Maganin Ciwo Mara A Lokacin Al’ada

 

Mabiya BBC Hausa a shafin Intagram fiye da 400 suka yi tsokaci kan wannan labari inda ra’ayoyinsu suka sha bamban a kan dora alhakin raguwar arzikin Dangote kan gwamnatin Shugaba Buhari.

Leave A Reply

Your email address will not be published.