GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Bai Kamata INEC Ta Fake Da Cewa Zabe Bai Kammala Ba Kawai A Rika Yiwa Jama’a Wala-Wala – Sunday Karimi

Bai Kamata INEC Ta Fake Da Cewa Zabe Bai Kammala Ba Kawai A Rika Yiwa Jama'a Wala-Wala - Sunday Karimi

37

- Advertisement -

Dan majalisar wakilan Nijeriya, Sunday Karimi, mai wakiltar Kogi, ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da kada ta yi amfani da damar bayyana zabe a matsayin wanda bai kammala ba, wajen yi wa al’umma wala-wala bayan sun zabi wadanda suke so a zabukkan da aka gudanar a makon da ya gabata….

 

Karanta: Masana Sun Gargadi Masu Ciwon Ido Da Su Guji Amfani Da Ruwan Albasa

 

Mambobin majalisar wakilan sun bukaci hukumar zaben da ta kasance mai bin dokokin kasa sau da kafa, sannan su taimakawa dukkan jam’iyyu da ‘yan siyasa da basu amince da sakamakon zabukka zuwa kotunan zabe da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’ummar kasa gaba daya.

 

Karanta: Kashi 6 Cikin 10 Na Matan Ƙasar Nan, Su Na Fama Da Taɓin Hankali – Masana

 

Dan majalisar ya koka da yadda yawan ayyana zabukka a matsayin wadanda basu kammala ya sa ake yi wa hukumar zaben kallon hadirin kaji, har ma ta kai wasu sun sauya wa hukumar suna daga mai zaman kanta zuwa mai ayyana zabukka a matsayin wadanda basu kammala ba.

 

Karanta: Zaben Gwamnan Jahar Sokoto: Mata Sun Yin Zanga-zangar Lumana (Hotuna)

Leave A Reply

Your email address will not be published.