GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Bambancin Da Ke Tsakanin Da Miji Da Mace – Daga Farfesa Murtadha

Bambancin Da Ke Tsakanin Da Miji Da Mace - Daga Farfesa Murtadha

23

- Advertisement -

 

Bambancin Halitta:

Namiji na da babban jiki, mace na da qaramin jiki. Namiji ya fi mace tsawo a galuban lokuta. Yanayin jikin namiji ya fi qarfi. Yanayin jikin mace ya fi sulbi. Muryar namiji tana da qarfi. Muryar mace tana da taushi. Jikin mace ya fi saurin bunqasa a kan na namiji, har masana a duniya ma sun yarda cewa dan tayi mace da ke cikin mahaifa ya fi saurin girma a kan dan tayi namiji irinsa. Mace tana riga namiji isa ga shekarun balaga, kuma tana riga shi daina haihuwa. Jikin mace ya fi na namiji qarfin garkuwar hana cututtuka shiga. Mace takan riga namiji fara iya magana. Yanayin qwaqwalwar namiji a halitta ta fi ta mace fadi, amma kuma bisa la’akari da kwatancen girman jikin kowanensu, to, qwaqwalwar macen ta fi. Wurin numfashin namiji ya fi na mace qarfin shaqar iska. Bugun zuciyar mace ya fi sauri a kan na namiji.

 

Karanta: Dalilan Da Yasa Muke Taka Rawa a Zabukan Nijeriya – Rundunar Soji

 

Bambancin Tunani:

Namiji ya fi ba wa ayyukan qarfi muhimmanci, kamar farauta da makamantansu a kan mace. Shu’urin namiji ya fi karkata ga harkokin qarfi irin yaqi da makamantansu. Shu’urin mace ya fi son zaman lafiya da lumana. Namiji ya fi karkata ga fusata da gardaddami. Mace ta fi karkata ga shiru-shiru da natsuwa. Mace, a wurin daukar mataki takan kauce wa amfani da qarfi, gare ta ko ga waninta. Wannan ne ya sa rahotannin kisan-kai suka fi yawa a tsakanin maza a kan mata. In har ma za a yi kisan-kan ne, namiji ya fi daukar matakin gaggawa, misali yakan dauki bindiga ya harbe kansa, ko ya rataye kansa, ko ya fado daga dogon gini ko tsauni. Ita kuwa mace ta gwammace ta sha guba ta mace abinta.

 

Karanta: Asiri: An Gano Sunan Gwamna El-rufai Kulle Cikin Likkafani A Makabarta (Hotuna)

 

Shu’urin mace ya fi saurin motsawa a kan na namiji. Hamasarta ta fi ta namiji saurin zabura ga abin farin ciki ko na baqin ciki. Namiji ya fi mace rashin saurin fizguwa ga farin ciki ko baqin ciki. Mace ta fi namiji son kyau da ado da qyale-qyale. Mace ta fi namiji saurin canza tunani ko ra’ayi. Mace ta fi namiji taka-tsantsan, ta fi shi son al’adu/addini, kuma ta fi shi surutu. Tunanin mace ya fi na namiji tausayi, ana iya ganin haka tun daga yarintarta. Mace ta fi namiji damuwa da halin da iyali ke ciki, kuma hankalinta ya fi nasa ba wa gida muhimmanci ba tare da ma ta san tana yi ba. A harkokin da suka shafi aiki da qwaqwalwa da hankali, mace ba za ta iya kwatanta kanta da namiji ba. Amma a harkar adabi, da dukkan harkokin da suka shafi kwalliya da qawa, mace ba a bayan namiji take ba. Namiji ya fi mace ikon kiyaye sirri, yana kiyaye sirrori ababen qi a qirjinsa fiye da mace. Wannan ne ya sa maza suka fi mata fama da cutukan da suka shafi tunani kamar hawan jini da makamantansu.

 

Karanta: An Kama Kasurgumin Dan Ta’addan Dake Haddasa Rikicin Garin Kasuwar Magani A Kaduna

 

Bambancin Yadda Kowannensu Yake Ga Dan Uwansa:

Namiji bawan sha’awarsa ne, mace kuma ta fi iya riqe kanta a soyayya ga namiji. Namiji, galibi yana son mace ne domin tana birge shi. Amma mace, galibi tana son namiji ne yayin da ta karanci qimarsa a wurinta. Namiji yana son mallakar mace ta hanyar iko. Mace tana son mallakar namiji ta hanyar yin tasiri a zuciyarsa. Namiji na da sha’awar ya rungume mace. Mace na da sha’awar namiji ya rungume ta. Mace tana son ganin sadaukantaka da qarfin hali a wurin namiji. Namiji na son ganin diri da kyawun halitta a wurin mace. Mace tana son ganin goyon bayan namiji gare ta, hakan yana da muhimmanci sosai a gare ta. Mace ta fi namiji ikon mallakar sha’awarta. Sha’awar namiji tana da zabura. Sha’awar mace kuwa sai an tsokano ta.

 

Daga: Farfesa Murtadha Mutahhari

______________________________________________
Tsakure daga littafin The Rights of Women In Islam, na Farfesa Murtadha Mutahhari. Na kawo shi ne domin taya mata murnar wannan Rana ta Mata ta Duniya tare da fatan mu da su za mu qara fahimtar juna don mu zauna cikin lafiya ba tare da sake-sake ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.