GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Cin Amana: Mijina Ya Man Duka Don Ban Gaida Amaryarsa Ba – Uwargida Ta Fadawa Kotu

Cin Amana: Mijina Ya Man Duka Don Ban Gaida Amaryarsa Ba - Uwargida Ta Fadawa Kotu

64

- Advertisement -

Wata mata mai matsakaicin shekaru, Zainab Ahmed, a jiya Talata ta gurfanar da mijinta, Oare Abdulrazak, a gaban kotun shari’ar musulunci ta biyu da ke zamanta a Magajin Gari, Kaduna, bisa zargin cin zarafi.

 

Kamfanin dillancin labarai ta Nijeriya, NAN, ya rawaito cewa matar da ke zaune a unguwar Hayin Dan-Bushiya, ta fadawa kotun cewa, mijinta Abdulrazak ya yi mata dan karen duka kawai wai don bata gaishe da amaryarsa ba a lokacin da suka hadu a kasuwa.

 

Karanta: Matsafa Sun Yiwa Wasu Kananan Yara Yankar Gunduwa-gunduwa

 

“Wannan ba shi ne karo na farko da ya ke yi min dukan tsiya ba. Hasali ma dai wannan shi ne karo na uku da ya ke lakada min duka akan matarsa. Na yi kokarin na yi masa bayanin abinda ya faru amma sai ya ki ya saurare ni,” inji Zainab

 

Zainab ta kara da cewa, mijinta sam baya nuna mata so da kauna a duk lokacin da ya ke dakinta, inda ta roki kotu da ta raba aurensu.

 

Karanta: Wata Mata Ta Haihu A Wajen Gangamin Taron Yankin Neman Zaben PDP

 

A ta bakin Abdulrazak wanda ke da mata 3, ya bayyana cewa shi fa sau daya ya taba dukan Zainab kuma ma ya yi nadama ya neni yafiyarta.

 

Mai shari’a Malam Musa Sa’ad-Goma bayan sauraron Zainab da Abdulrazk, ya umarce su da su gabatar da wakilansu a gaban kotu a zama na gaba don a yi tubkar hanci.

 

Karanta: ‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Abia

 

An kuma daga sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu, 2019.

Leave A Reply

Your email address will not be published.