GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Cuttuka 20 Da Shuwaka Ke Warkarwa A Jikin Dan Adam

Cuttuka 20 Da Shuwaka Ke Warkarwa A Jikin Dan Adam

267

- Advertisement -

Shuwaka wata ciyawa ce mai launin kore wacce ta ke girma a sassa daban-daban a Kasashen Nahiyar Afrika da ma Nahiyar Turai, har ya zuwa wasu yankuna na Kasashen Larabawa.

 

Komai na wannan ciyawar kama daga ganyenta, Saiwarta, da itaciyarta, Kabilar Igbo suna amfani da ganyen su yi abinci musamman miya, su kuma Yarbawa sun Dauki Shuwaka a matsayin magani wanda suka tarar kakanninsu na amfani da ita tun asali.

 

Karanta: 2019: Dalilin Da Ya Sa Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Ba Ta Yiwa Buhari Kamfen

 

A Kasar Hausa kuma, mata masu jego ne suka fi yawan amfani da shuwaka da mata masu shayarwa.

 

Da dama abin da wasu suka Dauki shuwaka kayan matane kawai, a dalilin haka yasa na zurfafa bincike a kan shuwaka da kuma yin rubutu na musamman a kan alfanun da take da shi ga lafiyar al’umma.

 

Karanta: Taron Atiku: ‘Yan Bangar Siyasa Sun Hallaka Wani Bawan Allah A Kaduna (Hoto)

 

Maganin Da Shuwaka Ke Yi A jikin Dan-Adam Suna Kamar Haka:

1. Shuwaka Na Wanke Hanta Daga Kwayoyin Cuta, Hanta ita ce abu mafi nauyi a cikin jikin Dan-Adam, inda hantar babban mutum ke da nauyin kilogram 1 zuwa 3 waton. ZuKar suga da kwankwadar giya da shan magungunna barkatai na illata hanta, wanda kusan duk abin da ya shafi hantar mutum to a haKiKa jiki zai fuskanci barazanar kamuwa da cutuka.

2. Shuwaka na taimakawa Koda sosai wajen karfafa aikinta, Koda wata muhimmiyar halittace da ke aikin fitar da duk wasu abubuwa marasa amfani daga cikin jiki, kamar fitsari.

 

Karanta: Amfanin Aya 7 Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

 

3. Idan kana fama da yawan tunani to sai a tace shuwaka a sanya Dan garin dabino kadan sai a zuba zuma a sha kofi Daya a kullum, KwaKwalwa za ta washe.

4. Shuwaka na maganin kasala marar misaltuwa, A nemi ganyen shuwaka a sabe a sha lita Daya da safe haka za a maimaita da yamma, a yi haka na tsawon wata Daya.

5. Idan an ci wani abinci wanda ya lalata ciki to a sha ruwan shuwaka, ko kuma rashin cin abinci a Koshi shima sai a sha shuwaka.

 

Karanta: Bidiyo: Yadda Ake Hada Kunun Aya Mai Dan Karen Dadi (Yana Kara Lafiya)

 

6. Gudawa ga yaran da ke shan nono a saboda rikicewar nonon sai uwar ta tace shuwaka ta sha a sanda za ta kwanta, haka idan gari ya waye za ta sha.

7. Shuwaka na wanke dattin ciki.

8. Tana maganin tsutsar ciki.

9. Duk wanda ke bahaya da kyar ko mai tauri ya dinga shan ruwan shuwaka.

10. Duk mai fama da rashin bacci ya dinga shan shuwaka.

11. Yana maganin Kumburin ciki da zafin ciki.

12. basir mai sa kumburin dubura.

 

Karanta: Dakarun Sojojin Nijeriya Sun Kashe ‘Yan Bindiga 58 A Zamfara

 

13. Yana maganin zafin ciki (internal heat) ko kaga kana bayan gari amma hayaKi na tashi a ciki.

14. Karin ruwan nono ga mata masu shayarwa a nan sai a riKa yin kununta a na sha.

15. Tana tsaftace nonon da ya gurBbace.

16. Tana warkar Cututtukan fata sai a saBe ta a shafawa wajen da ke da matsalar.

17. Mai fama da Maleriya ya riKa sha a na surace da ruwanta ko wanka da shi, amma da duminsa.

18. Maganin cututtukan Kwayoyin halitta ce ‘ANTIBIOTIC’ ina nufin tana kashe Kwayoyin cuta.

 

Karanta: (Gargadi) Maganin Karfin Mazakuta Ya Sa Wani Makancewa Da Hauka

 

19. Idan kana neman ka tsaftace cikinka daga yawan tugugi da tsuwa to sai ka gyara shuwaka ka sha.

20. Mata masu fama da matsalar rashin haihuwa to a fake amfani da shuwaka.

Leave A Reply

Your email address will not be published.