GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Da Duminta: EFCC Ta Damke Tsohon Gwamnan Jihar Kebbi (HOTO)

Da Duminta: EFCC Ta Damke Tsohon Gwamnan Jihar Kebbi (HOTO)

111

- Advertisement -

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kebbi, Usman Saidu Dakingari a gaban kotu bisa zargin halasta kudin haramun.

 

Karanta wannan: An Tasa Keyar Wani Matashi Zuwa Gidan Yari Kan Ya Sace Sachet Na Madara A Abuja

 

Kakakin hukumar, Tony Orilade ne ya bayyana haka inda ya ce sun gurfanar da Dakingari da wasu mutum biyu a kotu bisa zargin aikata laifuka 13, ciki har da hada baki wurin aikata laifi da halasta kudin haramun da suka kai N450m.

 

Karanta wannan: Yakar Ta’adanci: An Nada Sabbin Kwamandojin Sojojin Nijeriya [Ga Jerin Sunayensu]

 

An gurfanar da mutanen uku ne a babbar kotun tarayya da ke Kebbi wacce mai shari’a Basse Onu ke jagoranta.

 

Karanta wannan: Siyasa: “Allah Sai Ya Azabtar Da Obasanjo A Kan Marawa Atiku Baya” – Oshiomole

 

Ana zargin su ukun Dakingari da Sunday Dogonyaro da kuma Garba Rabiu Kamba da laifin karbar N450m wadanda wani kaso ne cikin $115m da tsohuwar ministar man fetur ta kasar Deizani Alison-Madueke ta rabawa ‘yan siyasa gabanin zaben 2015 da zummar sauya alakar zaben.

Sai dai mutanen sun ce basu aikata laifin ba inda alkali Onu ya bukaci EFCC ta ci gaba da tsare su sannan ya dage sauraren karar zuwa ranar goma ga watan Disamba domin yin hukuncin kan yiwuwar bayar da belinsu.

 

Ga hotuna a kasa;

Leave A Reply

Your email address will not be published.