GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Dakin Girkin Sarauniya: Yadda Ake Girka Miyar Karas

Dakin Girkin Sarauniya: Yadda Ake Girka Miyar Karas

178

- Advertisement -

Akwai hanyoyi da dama da uwargida zata iya bullowa tsadar tumatirin da ya addabe mu a yanzu. Daya daga cikin wadannan hanyoyin shine amfani da karas wajen yin miya. Miyar karas tana da kayatarwa sosai kuma zata iya maye gurbin miyar tumatiri wajen cin Shinkafa, Doya ,Taliya da sauransu.

 

Karanta: Hanyoyin Gujewa Fitowar Furfura A Jikin Dan Adam

 

Abubuwan Bukata

 

1.Karas

2.Tattasai

3.Tarugu

4. Albasa

5. Citta

6. Tafarnuwa

7. Naman sa ko na kaza

 

Karanta: Jonathan Ya Karyata Ficewa Daga Jam’iyyar PDP

 

Yadda Ake Hadawa

 

Da farko zaki dafa naman ki da kayan kamshi da kayan dandano da Albasa. Idan ya dahu sai ki juye ruwan ki ajiye a gefe, shi kuma naman ki soya shi sama sama.

 

Dagan nan sai ki hada Tattasai, Tarugu, Albasa, Citta, Tafarnuwa da Karas din ki nika su a injin nika ko kuma ki kankare shi da grater, bangaren da yake da kananan hudoji.

 

Karanta: Yadda Kuka Wiwi Ke Inganta Lafiya Da Magance Damuwa

 

Sannan sai ki soya Manja/Man gyada, in ya soyu sai ki zuba abunda kika nika ki barshi ya soyu sosai, ki kara kayan kamshi da kayan dandano kadan saboda akwai a cikin ruwan naman ki.

 

Idan ya soyu sai ki kwara ruwan naman ki da soyayyen naman ki barshi ya zabalbala.

 

Miya ta sauka. Aci dadi lafiya

Leave A Reply

Your email address will not be published.