GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Dalilan Da Kansa Wasu Samari Suke Gujewa Kyauwawan ‘Yan Mata

Dalilan Da Kansa Wasu Samari Suke Gujewa Kyauwawan 'Yan Mata

157

- Advertisement -

Kowane dan Adam ya kan so ya samu kyakyawar abokin zama amma sai a yayin da suka kusanci juna da kyau da kyau za su gane gaskiyar bayani a kan mutanen da ke da kyaun halitta a fuska. Kun taba tsayawa kun yi tunani a kan dalilin da ya sa hadaddun samari ba su son ‘yan kyauwawan mata? Ba wai kawai don suna duba kyaun zuciya bane; a dan wani tsawon lokaci na zamantakewa su kan gane wasu abubuwa ne game da su.

 

Wasu Irin Halaya Ne Kyauwawan ‘Yan Mata Ke Yawan Barazana Da Shi?

 

Karanta: 2019: Zan Baiwa Mata Mukamai Daidai Da Yawansu A Nijeriya – Atiku

 

MAFI YAWANCI ‘YAN MATA SUNA ALFAHARIN CEWA KYAUN SU ABUN JARI NE A GARE SU

Mafi yawancin kyauwawan ‘yan mata suna ji da kansu. Sun san da cewa suna da kyau, sun san da cewa mutane da dama na sha’awarsu, hakan ya kan ja hankalinsu musamman yadda suka yi la’akari da cewa kowane namiji da ke son yin soyayya da su sai ya kashe kudi sosai kafin ya same su. Ba kowane namiji ya yadda da hakan ba, hakan kan sa mazajen kwarai su guje su.

 

WASU KYAUWAWAN ‘YAN MATA BA SU DA HALI MAI KYAU

 

Don sun san suna da kyau sannin hakan ya kan rinjaye su, hakan sai ya sa su suna kaskantar da mazajen da ke son su. Saboda babu wanda ya ke so ya ga an kaskantar da shi saboda kawai yana son wata ‘ya mace, hakan ya kansa maza su guje irin wannan matan.

 

Karanta: Alamomin Gane Maza ‘Yan Luwadi (Hoto)

 

WASU ‘YAN MATAN AKWAI SUN NUNA BAMBANCI

 

A ajiye kudi a gefe, ba kowane kyakyawar mace ke kallon namiji ba idan har bai hadu ba kamar yadda suke. Mafi yawancin maza sun san da haka, shi yasa ba su ma damun kansu a irin wannan lamarin.

 

MAFI YAWANCIN KYAUWAWAN ‘YAN MATA SUN CIKA WASA DA HANKALIN MAZA

 

Abun gaskiya  a nan shine yawancin kyauwawan ‘yan mata suna yawan wasa da hankalin maza, da wuya maza ke gane lokacin da suke son yin soyayya don aure ko kuma kawai soyayya bata lokacin juna ne kawai. Mafi yawancin maza sukan yanke hukunci cewa irin wadannan mata suna mazajen da za su aura, shi yasa kawai maza kan guje su.

 

Karanta: Sunayen Sinadaran Girki A Turanci Da Hausa

 

CHANFI A KAN ZAMA KYAUWAWAR MACE

 

Mafi yawancin maza sun su kan dauke kyauwawan ‘yan mata a matsayin mata marasa ilimi. Duk da cewa ba gaskiya bane, amma wata sa’a ya kan zanto gaskiya. Hakazalika, bai dace ana fadan haka ba ga sauran mata kyauwawa masu ilimi.

 

RASHIN TABBACI DA RIKON AMANA

Dalilin da ya sa wasu mazan kan share kyauwawan ‘yan mata shine ba za su taba samun kwanciyan hankali ba don a koda yaushe a daudau suke kada wani maikudi ya kwace masu budurwa wata rana. Hakan wata sa’a ba gaskiya bane, amma maza da dama kan fuskanci irin wannan matsala, shi yasa su kan guje yin soyayya da kyauwawan ‘yan mata

Leave A Reply

Your email address will not be published.