GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Dalilin Da Ya Sa Na Yiwa Mahaifiyata Tare Da Surukata Fyade – Inji Wani Manomi

Dalilin Da Ya Sa Na Yiwa Mahaifiyata Tare Da Surukata Fyade - Inji Wani Manomi

73

- Advertisement -

Wani manomi dan shekaru, 32, daga jihar Kaduna, wanda aka bayyana sunarsa a matsayin, Sehakru David, ya furta cewa ya yiwa mahaifiyarsa tare da surukansa fyade. inda ya ce jinnu ne suka saka masa son yin jima’i da tsoffin mata.

Jami’in tsaro na ‘yan sanda masu aiki a karkashin Sifeto Janar na ‘yan sanda na sashen leken sirri IRT suka cafke David.

 

Karanta wannan:  Wani Matashi Ya Yiwa Wata Akuya Mai Ciki Fyade

 

An cafke wanda ake zargi ne bayan an kama shi da hannu a harkar fashi da makami tare da yiwa mata fyade a karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna.

Dan shekaru 32 ya furta cewa ya yiwa mahaifiyarsa tare da surukansa fyade wadanda shekarunsu ke tsakanin 65 zuwa 70.

 

David ya furtawa jami’in IRT cewa matarsa ta rabu da shi sannan ta auri wani mutum saboda halinsa na yiwa tsoffin mata fyade.

 

 

Dan kungiyar sintirin ya bayyana shi David a matsayin dan ta’adda wanda ya shahara a yiwa tsoffin mata mazauna Manchie da kewaye fyade.

 

Mazauna yankin suka kai karar wanda ake zargi ga ‘yan kungiyar sinitiri na yankin sau 2, a kan cewa David ya yiwa mahaifiyarsa tare da surukkansa fyade.

 

A yayin da ya ke furta laifukan da ya aikata, David ya ce, “Ni manomi ne sannan na taba aure amma mata na ta rabu da ni sakamakon abun kunya da ni ke aikatawa na yiwa tsoffin mata fyade.

 

Karanta wannan: Tsoho Dan Shekaru 50 Ya Yiwa Wata Budurwar Fyade A Jihar Gombe

 

“Ban sani ko asiri aka yi ma ni amma a duk lokacin da na sha giya wani jinnu ya kan shiga jikina sannan sai na fara yawo neman mata. An taba ma ni dukan tsiya sau da dama saboda hakan amma na kasa bari yin hakan da zaran na bugu.

 

“Na yiwa mahaifiyata fyade a lokacin bikin gargajiyar Moroha bayan na sha giya. Ban samu wata tsohuwa ba a wannan ranar sai da na isa gida na cimma mahaifiyata na ma ta fyade.

 

“Mahaifiyata ta ihu neman agaji, hakan ya sa makwabtan mu suka fito daga gidajensu don kawo agaji. Kowa sai ya ga cewa na buigu ne, a lokacin da na dawo haiyaci na sai na roki mahaifiyata gafara sannan ta yafe ma ni.

 

“A lokacin da tsohuwar mata ta samu labarin hakan sai ta ji haushi ta bar gidan na mu ta koma gidan iyayenta kafin ta samu wani mijin da ya aure ta.

 

Karanta wannan: Dan Shekaru 21 Yayi Jima’i Da Gawar Mahaifiyarsa Bayan Ya Kashe Ta

 

“Ba’a dade da yin hakan ba, na halarci wani bikin gargajiya wanda aka gudanar a kauyen mata na wanda ake kira da suna Mahuta sannan na bugu. Da dare yayi  sai na tafi zuwa gidan mahaifiyar tsohuwar mata na na cimma ma ta tana bacci. Sai na yiwa suruka na fyade sai mutane suka zo suka zo suka kama.

 

“Mutane sun yi ma ni sukan tsoya kafin aka bar ni na tafi. Ban san abunda ke faruwa da ni ba idan har na bugu. Wani jinnu kawai ya kan shiga jikina na ya sa ma ni son yiwa tsoffin mata fyade.

Leave A Reply

Your email address will not be published.