GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Dalilin Da Ya Sa Nake Lalata Da ‘Ya’yana Hudu – Uba

Dalilin Da Ya Sa Nake Lalata Da ‘Ya’yana Hudu – Uba

142

- Advertisement -

Wani mutumi mai suna Rashidi da ke zaune a Sango-Ota a jahar Ogun ya dade ya na lalata da ‘yayanshi hudu mata masu shekaru 26, 23,19 da 14.

 

Karanta: An Sace Mutane Sama Da 30 A Kwanaki Biyu Kacal A Hanyar Kaduna-Abuja

 

A yanzu haka mutumin mai shekaru 47 a duniya ya shiga hannun ‘yan sanda bayan da suka samu rahotanni game da lamarin.

‘Yan sandan sun gano cewa matar mutumin kuma mahaifiyar yaran ta san cewa wannan lamari na faruwa amma ba ta dauki mataki a kai ba.

Hasali ma, ‘yayan hudu da matar sun yi ta rokon ‘yan sandan tare da yin kuka akan cewa a saki mahaifinsu, inda suka ce ba a hayyacinsa ya ke aikata wannan abu ba.

Shi ma mutumin cikin hawaye ya fadawa ‘yan sanda cewa asiri aka yi masa, domin kuwa a duk lokacin da ya aikata wannan abu, ba a hankalinsa ya ke ba. Sai bayan kamar awanni uku tukunna sai ya dawo hayyacinsa.

 

Karanta: Kotu Ta Yankewa Wasu Matasa 4 Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Laifin Sata

 

Rashidi ya fadawa ‘yan sandan cewa wata murya ya ke ji na fada masa ya aikata wannan abu, kuma a duk lokacin da muryar ta fara yi masa magana, sai ya fita a hayyacinsa.

Suma ‘ya’yan hudu sun fadawa ‘yan sandan cewa asiri bai barsu ba, domin kuwa a duk lokacin da mahaifin ya ce su tube kayansu, ba su iya yi masa gardama.

Sai dai sun ce sun dade suna nema wa mahaifin magani amma ba a yi dace ba.

 

Karanta: Facebook Na Shirin Fito Fa Hanyar Da Mutane Za Su Gane Masu Sonsu A Boye

 

Sun roki ‘yan sandan akan cewa kar su kai mahaifinsu kotu, domin ba tonon asiri ya ke bukata ba, magani ya ke bukata.

Leave A Reply

Your email address will not be published.