GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Dalilin Da Yasa Aka Hana Tashe A Jihar Kano

Dalilin Da Yasa Aka Hana Tashe A Jihar Kano

12

- Advertisement -

A daidai lokacin da azumin watan Ramadana yazo tsakiya, wasu jihohin arewa sun fara tashe, wanda ya kasance daya daga cikin al’adun kasar Hausa a cikin wata mai tsarki.

 

Karanta: Amfanin Shan Ruwan Kwakwa Guda 12 Da Zai Baku Mamaki

 

Bisa al’da da zaran azumi ya kai tsakiya, kananan yara da ma wasu manya kan fita yin wasannin barkwanci da sunan tashe, inda za a dunga basu kyaututtuka.

Sai dai a jihar Kano wadda take a matsayin daya daga cikin manyan yankuna na kasar Hausa, abin ya sha bambam. Domin kuwa kamar yadda ta faru a wasu shekarun baya, a wannan karo ma hukumomi a jihar sun haramta gudanar da wannan al’ada mai dinbin tarihi.

Tuni rundunar ‘yan sandan jihar ta Kano ta ce za ta dauki tsattsauran mataki kan duk wani da aka kama ya taka dokar hana yin tashe a jihar.

Kakakin yan sandan jihar, DSP Haruna Kyawa ya ce jami’an ‘yan sanda na yin sintiri a cikin dare domin tabbatar da cewa ba a bari masu neman tayar da fitina sun cimma burinsu ba.

Ya ce: “ba wai tashen ne laifi ba, a’a. Amma bata gari da suke bin ‘yan tashen suke fakewa da haka suke yin kwace da sauran miyagun laifi shi ne ba ma so.”

 

Karanta: Babu Wanda Ya Isa Ya Hana A Rantsar Da Ni – Aminu Tambuwal

 

Ya kuma jadadda cewa jami’ansu zasu dunga sintiri a kewayen jihar tun daga lokacin sallar magariba zuwa karfe goma na dare don kama wadanda karya doka.

Leave A Reply

Your email address will not be published.