GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Dan Majalisan Neja Ya Gina Gadaje, Da Tituna Tare Kwalbatai Da Asibitoci A Mazabansa (Hotuna)

Dan Majalisan Neja Ya Gina Gadaje, Da Tituna Tare Kwalbatai Da Asibitoci A Mazabansa (Hotuna)

152

- Advertisement -

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu a majalisar wakilai na kasa, Rep. Abdullahi Idris Garba (AIG) wanda aka fi sani da suna ‘MAI SOLAR’ ya gina gadaje, da tituna tare da kwalbatai a mazabansa.

 

Karanta: Yadda Ake Amfani Da Kwai Wajen Maganin Karfin Mazakuta

 

A yayin da wakilin mu yayi hira da dan majalisan a wayar hannu dan majalisan ya bayyana cewa “ayyukar da ya ke aiwatarwa a fadin mazabun nasa sun kasance cikin kudirorinsa da samar da ci gaba ga al’ummar mazabarsa tare da kuma cika alkawarinsa.”

 

Dan majalisa Abdullahi ya ce “idan har aikin ci gaba ne a yanzu ya fara sannan kuma ya kara da cewa har ila yanzu wakilansa na nan suna yawo lungu-lungu a duk fadin mazabunsa don gudanar da bincike a wurare daban-daban inda suka cancanci a masu ayyuka irin wanda yankinsu ke bukata.”

 

Ya ce “za ka ga wasu wurare suna da hanyoyi amma babu isashen tsabtataccen ruwan sha a yankinsu wasu kuma wuraren akwau ruwan sha amma babu hanyoyi, hakan ya sa mu ke aika wakili yankunan daban daban a duk fadin mazabar tawa domin gano irin wannan abubuwan don magance matsalar da yankunan ke fama da shi. Yin hakan zai sa aiki a yiwa kowane yankin iya aiki da ta ke bukata cikin tsari.”

 

Karanta: Rep. Abdullahi Ya Horas Da Wasu Matasa Daga Cikin Jami’ansa Masu Kula Da Kafofin Sada Zumuntansa

 

A karshe dai dan majalisan yayi kira ga al’umma mazabansa da su ci gaba da hakuri tare da marawa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari baya domin Buhari shugaba mai kishin kasa sannan kuma mai son ganin ci gaban kasar Najeriya ga baki daya.

 

A cikin ayyukar da dan majalisar ya bada kwangila sun hada gina gadaje, da titin akalla kilomita 2 da kuma kwalbatai a unguwa daban daban da ke fadin mazabarsa musamman inda zaizayar ta addaba, da kuma asibitoci a kauyukan da ke da nisa da garuruwan da ke da manya-manyan asibitoci.

 

Ga hotuna a kasa;

Leave A Reply

Your email address will not be published.