GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Duk Da Taron Dangi Sai Da Kwankwaso Ya Kai Gwamnatin Ganduje Ƙasa A Kano – Nasiru Sule Garo

Duk Da Taron Dangi Sai Da Kwankwaso Ya Kai Gwamnatin Ganduje Ƙasa A Kano – Nasiru Sule Garo

76

- Advertisement -

Ɗan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Gwarzo da Kabo a majalisar wakilai ta ƙasa Nasiru Sule Garo, ya bayyana cewa duk da taron dangin da aka yiwa Shugaban ɗariƙar Kwankwasiyya amma sai da maigidan nasu, Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya kai Gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ƙasa.

 

Karanta: Ku Tashi Da Azumi Domin Samun Nasarar Gwamna Ganduje – In Ji Faizu Alfindiki

 

Nasiru Sule Garo ya ce duk masu adawa da kyakyawar zuciya irin ta Kwankwaso to haƙiƙa sun makaro, domin a cewarsa Kwankwaso gwamnan na jihar Kano yayi masu fintinkau.

 

Karanta: Babban Hadimin Ganduje Ya Ajiye Aikinsa Sabo Da Gwamnan Ya Ƙi Karɓar Ƙaddara

 

Nasiru Garo ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Leadership Nasiru wanda ya fadi zaben dan majalisar wakilai wanda ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu yace shi baya bakin ciki ga faduwar da yayi a zabe domin cewarsa Allah ne mai bayar da mulki.

 

 

Karanta: Zaben Kano: Ina Da Tabbacin Samun Nasarar Lashe Zaɓen Da Za’a Sake – In Ji Gwamna Ganduje

 

A ƙarshe ya ce kamar yadda aka sani shi bai shiga siyasa ko a mutu ko ayi rai ba, musamman ganin irin ƙaunar da al’ummar da ya ke wakilta ke yi masa, wannan tasa sakamakon zaɓen da ya bayyana ya kalle shi tare da kyautatawa Allah zato.

Leave A Reply

Your email address will not be published.