GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

EFCC: Kotu Ta Baiwa Shekarau Iznin Tafiya Umara

EFCC: Kotu Ta Baiwa Shekarau Iznin Tafiya Umara

36

- Advertisement -

 

 

Kotun tarayya ta mai shari’a Lewis Allogoa da ke sauraron karar da EFCC ta shigar da zababben sanata na Kano Central, Mallam Ibrahim Shekarau da Ambasada Aminu Wali da Injiniya Mansur Ahmed,ta bada izinin ya je ya yi ibadar Umara a cikin wannan watan Ramadana in Allah ya kaimu.

 

Karanta: Dandazon Ƙudan Zuma Ya Kashe Wani Jami’in Hukumar Kwastan

 

A yau a zaman da aka yi, wanda shi ne zama na 11, kotu ta baiwa akawunta izinin ya baiwa Mallam Shekarau fasfo dinsa domin ya je kasa mai tsarki.

 

EFCC tana ci gaba da kawo shaidun da ta dogara da su wajen shigar da korafinta, zuwa jiya ta gabatar da shaidu guda hudu, saura shaida guda daya.

 

 

Karanta: Shugaba Buhari Makaryaci Ne – Inji Reno Omokri

 

Tunda shaidu suka fara bada bahasinsu babu ko mutum daya da ya ambaci sunan Mallam Shekarau, kuma ma’aikatan banki sun gaya wa kotu cewa duk ma’amalolin da aka yi ba su sabawa ka’idojin aikin banki.

Leave A Reply

Your email address will not be published.