GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Every-woman: Mahaifiya Makarantar Al’umma

Every-woman: Mahaifiya Makarantar Al'umma

16

- Advertisement -

Sau da yawa akan dauka in mace ta haihu ta gama wahala kenan, wadanda suka zaci haka to ba haka bane.

Da zarar dai mace ta haihu, zata ji da ta dau wani kayane mai nauyin gaske aka sauqe mata, zata jita sakayau, in ta tashi tsaye ma za a iya daukarta saboda rashin nauyi, sannan yawancin mata Suna haihuwa sai ciwon ciki yayi musu sallama, wannan ciwon cikin yakansa wasu Suma, wasu kuma basa suma amma yana iya fitar da mace daga hayyacinta, suyita sambatu saboda wahala suna shure-shure.

 

Karanta: EVERY-WOMAN: Your Husband, Your Paradise

 

Mata da yawa Dana tambayesu game da wannan ciwon cikin, cemin suka yi su sun gwammace ciwon naquda da wannan ciwon cikin domin yafi ciwon naquda gigitarwa.

 

Sannan kuma sau da yawa ba abunda zasu sha yayi musu sauqi, sai dai yayi iya yinsa ya daina don Kansa, kuma ba daqiqoqi ko mintoci ko awowi yake yi ya daina ba kuma kwanaki yake kafin ya daina.

 

Hakanan bayan ta haihu wata cuta ce kuma sabuwa da zata Shiga jinyarta, wannan jinyar da zata yi shi ake qira JEGO.

 

Karanta: Atiku Ya Fara Wallafa Hujjojin Zuwa Kotu

 

Wannan cuta da jinyace-jinyace da mahaifiya take ta faman yi, sau da yawa ya kan kasance don daukar dalibi daya daga cikin daliban makarantarta.

 

Wata za’a sameta tana da dalibai sama da goma a cikin makarantarta kuma ko wani dalibi sai da tayi fama kamar yadda muka yi bayani a baya, wani dalibin ma in ya tashi zuwa yazo da gardama har sai an yiwa malamar tashi aiki da wuqaqe kafin a Ciro shi.

 

Karanta: Jam’iyyar PDP Na Shirin Yamutsa Hazo A Najeriya

 

Anan zan dakata INSHA ALLAHU rubutu na gaba zamu ji yadda dalibin makaranta zai kasance a farkon darasin makarantar mahaifiyarsa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.