GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Everywoman: Mata Don Allah A Koyi Iya Yin Girki

Everywoman: Mata Don Allah A Koyi Iya Yin Girki

53

- Advertisement -

Duk macen da bata iya girki ba, ba kuďin taran mahaifinta kaďai ta yi hasara ba har da sadakin mijinta.🙄

 

🍲In ka ganta qalqal kamar da gaske. Surutu da zuba kamar an ‘balle tafki. Ga rashin kunya da zancen batsa kamar daga amurka ta sakko. Ta iya kashe shi da soyayyan hoho, tana nuna masa zai ji dadin aure. Sai kwalliyar banza da yangan iska, amma a girki 0%.

 

Karanta: Direba Make Da Ruwan Giya Ya Murkushe Yara 6 Har Lahira A Gombe

 

Wane ‘bacin rai da baqin ciki ya kai wulakanta cefanen miji, ta hanyar dafa masa jagwalgwalallen abinci? Wane takaici ya kai in zai dawo gida yana tunanin kwa’ben abincin ki. Wane kunya ya kai namiji ya ce dafa mun abu kaza, ki fara shiga dictionary neman ilimin da baki ajiye ba kuma baki bada ajiyansa ba.

 

Qanqanin abun da yaro ďan shekara 10 zai iya yi. A ce gandareriyar budurwa ‘yar 25 bata iya ba. Babu wani uzuri da zan bawa mace na bata iya girki ba. Kuma babu uzurin da zata bani da zai isa gamsar da ni.

 

Karanta: Maganin Radadi Da Zafin Ciwon Hakori

 

🍛Duniya ta waye, rayuwa yayi sauqi. An wuce lokacin ban iya ba, ko gidan mu ba su iya ba ne. Domin mazan zamanin nan sam-sam basa fahimta yaren ban sani ba. Yarinya tun da qimarki da mutunci KI KOMA KITCHEN!

🍚Domin abinci makami ne babba na yaqar sojojin qauna da soyayyan miji. Ki ci birnin zuciyar sa da yaqi, ki kafa gwamnatin ki.

Leave A Reply

Your email address will not be published.