GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Fadan Ƴan Daba Ya Haifar Da Rikici A Jos

Fadan Ƴan Daba Ya Haifar Da Rikici A Jos

92

- Advertisement -

 

 

Wasu matasa ƴan sara suka sun hallaka wani ɗan uwansu a dalilin wata jayayya da ta auku tsakaninsu a yankin unguwar Rukuba da ke cikin garin Jos, wanda a dalilin haka rikici ya balle tsakanin Musulmi da Kirista a anguwannin Dutse Uku, Jos Jarawa, Bauchi Ring Road da makwabtan yankuna.

 

Karanta: Mata Sun Fi Maza Rikon Amana, Domin Ba Za Su Yi Min Zagon Ƙasa Ba – Gwamna Ganduje

 

Kawo yanzu dai babu wani adadi na yawan rayukan da aka rasa ko hasarar dukiya da gidaje da aka yi. Wani mazaunin unguwar Dutse Uku, Umar Yunus, ya tabbatar da cewa, jami’an tsaro sun shawo kan lamarin, ko da yake har ya zuwa yammacin Lahadin nan ba a daina jin karar harbe-harbe a yankin ba.

 

Karanta: Hanyoyin Kariya Daga Saran Maciji

 

Sauran unguwannin cikin garin Jos dai na zaune lafiya, duk da yake akwai fargabar abin da zai iya biyowa bayan dare.

Leave A Reply

Your email address will not be published.