GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Gamyayyar Kungiyoyin Kwadago Na Kasa Za Su Shiga Yajin Aiki Na Duk Gari

Gamyayyar Kungiyoyin Kwadago Na Kasa Za Su Shiga Yajin Aiki Na Duk Gari

66

- Advertisement -

Kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), a jiya Litinin, ta tabbbatr da cewa za ta shiga yajin aiki na sai baba-ta-gani a ranar 8 ga watan Janairun, 2019 bayan da wa’adin da ta debawa gwamnati na 31 ga watan Disambar, 2018 ya cika a jiyan.

 

Karanta: Mafi Karancin Albashi: Abunda Ya Sa Jihohin Nijeriya Ba Za Su Iya Biyan N30,000 – Kungiyar Gwamnoni

 

Kungiyar ta bayar da wannan sanarwa ne jiya a jihar Legas a wani yunkuri nata na ganin cewa an hanzarta tabbatar da zartar da tsarin kunshin sabon mafi karancin albashi.

 

Karanta wannan: Makiyaya Sun Bankawa Gonar Shinkafar Gwamna Ortom Wuta

 

Sakatare Janar na kungiyar ta NLC, Kwamared Ozo-Eson ya shaidawa manema labarai cewa gamayyar kungiyoyin kwadago na NLC, TUC da ULC sun cimma matsayar shiga yajina aiki na duk gari a ranar 8 ga watan Janairu sakamakon kin aikewa majalisar wakilai kunshin sabon mafi karancin albashin da gwamnati ba ta yi ba.

 

Karanta: Amfanin Namijin Goro 12 Ga Lafiyar Dan-Adam

 

Ozo-Eson ya tabbatr da cewa gamayyar kungiyoyin kwadago za ta tabbatar da tsayawar al’amura a fadin kasar nan daga ranar 8 ga wata.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.