GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Gargadi: Masu Fama Da Ciwon Ido Su Guji Amfani Da Ruwan Albasa – Masana

Gargadi: Masu Fama Da Ciwon Ido Su Guji Amfani Da Ruwan Albasa - Masana

11

- Advertisement -

Babban Darekta mai kula da gudanarwar ma’aikatar lafiya na jihar Legas, Dakta Funmi Shokunbi, ta gargadi mutane da su guji amfani da ruwan albasa a yayin da suke fama da ciwon ido, ta yi wannan gargadin yau Laraba a yayin da ta gana da manema labarai a Legas.

 

Karanta: Kashi 6 Cikin 10 Na Matan Ƙasar Nan, Su Na Fama Da Taɓin Hankali – Masana

 

Likitar ta ce ba karamin kasada bane sanya duk wani abu a cikin idanu, muddin ba likita bane ya umarci mutum ya sanya shi a idanun sa, kuma hakan yana iya haifarwa da mutum wani nau’in ciwon ido da yake iya jawo makanta ta dindindin.

 

Karanta: Za Muyi Hukunci Mai Tsanani Ga Masu Siya Da Siyar Da Kuri’ar Su a Kano – ‘Yan Sanda

 

Amfani da ruwan albasa, ko fitsari, ko ruwan batir da sauran sinadarai wajen kokarin magance ciwon ido ba karamin kasada bane, yin hakan cike yake da ganganci, haka ma amfani da magungunan da ba likita bane ya yi umarni da ayi amfani da su yana da matsala, Inji Dakta Funmi.

 

Karanta: Wani Mutum Ya Sace Shanu 150 Ya Yanka Guda 50 a Ciki

 

Daktar ta kara da cewa; an fi samun wannan nau’in ciwon idon a kasashen nahiyar Afirka ne saboda tsabar gwanancewar mu a wajen kasada da ganganci da rayuwarmu, don haka shawarata shine da zarar ka ji baka ganewa idonka yi maza ka garzaya wajen likita domin samun kulawar da ta dace.

Leave A Reply

Your email address will not be published.