GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Hukumar INEC Ta Gano Mazabu 24 Da Zabe Ba Zai Iya Yiwu Ba A Jihar Yobe

Hukumar INEC Ta Gano Mazabu 24 Da Zabe Ba Zai Iya Yiwu Ba A Jihar Yobe

37

- Advertisement -

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce ta gano wasu mazabu har 24 a Jihar Yobe, wadanda saboda matsala ta tsaro, zabe ba zai yiwu ac gudanar da zabe a yankunan ba.

 

Kwamihinan Zabe na Jihar, Ahmad Makama ne ya bayyana haka a wani taron tattaunawa da juna a Damaturu, Jihar Yobe, a ranar Laraba.

 

Karanta: Miyagun Kwayoyi: Kwastam Ta Cafke Kwantenoni 40 Makare Da Tramol

 

Ya ce jami’an tsaro sun gano wasu yankuna a cikin kananan hukumomin Gulani, Gujba da Giedam cewa zabe ba zai yiwu a yankunan ba.

 

Makama ya ce INEC ta na tattaunawa da mazauna yankunan wadanda suka yanki rajisata domin sama musu mafitar yadda za a yi su yi zabe.

 

Karanta: Illar Ruwan Tsarkin Bayan Gida Idan Ya Taba Al’aura (Shawara Ga Mata)

 

Ya ce INEC na kokarin tabbatar da cewa duk wanda ya yanki rajista ya yi zabe. Don haka ta na tuntubar dukkan jam’iyyun siyasa domin a cimma matsaya daya ta inda mutanen mazabun da abin ya shafa za su jefa kuri’ar su.

 

Ya ce akwai katin rajisata 69,000 da har yau ba a karba ba a jihar Yobe.

 

Ya yi kira ga masu katin da su garzaya su karbi abin su domin samun damar jefa kuri’a a wannan zabe mai zuwa.

 

Karanta: Illar Yawan Amfani Da Magungunan Jima’i (Shawara Ga Maza)

 

A karshe ya bada tabbacin cewa akwai matakan tsaro sosai a sauran rmazabu 2.823 a fadin jihar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.