GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Jam’iyyun Adawan Kaduna Sun Yi Watsi Da Nasarar El Rufa’i

Jam’iyyun Adawan Kaduna Sun Yi Watsi Da Nasarar El Rufa’i

13

- Advertisement -

Da suke bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da suka kira a Kaduna, gamayyar jam’iyyun su 37 sun bayyana sakamakon da INEC ta fitar wanda ya baiwa El Rufa’i nasara a matsayin shirme abin dariya.

Karanta: Dalilin Sake Zaben Gwamnan Jahar Kano Zagaye Na Biyu

Alhaji Umar Ibrahim Mai Rakumi shine shugaban gamayyar Jam’iyyun, ya bayyana cewar suna da kwararan hujjoji wadanda suka tabbatar da cewar ba’a gudanar da zabe a wurare masu yawa ba wadanda suka hada da kananan hukumomin Zariya, da Igabi da Birnin Gwari da kananan hukumomin Giwa da Lere, da sauran wurare da dama a fadin jihar, ba’a yi amfani da na’urar Card Reader ba, sai dai kawai anyi dangwale ne kawai.

Karanta: Munyi Maraba Da Sakamakon Jihar Kano – Ganduje

‘Yan adawan sun cigaba da cewar, sama da Rumfunan zabe 650 da kuri’u sama da 400,000 aka soke duk dai domin a baiwa jam’iyya mai mulki ta APC dama.

Karanta: A Baiwa Duk Wanda Ya Ci Zaɓen Gwamna A Kano – In Ji Abdulmumin Jibrin Kofa

Bisa ga wadannan tarin hujjoji da muke dasu, muke tabbatar da cewa gamayyar Jam’iyyun mu 37 da ‘yan takara 18 da muke da su, mun yi watsi da nasarar da akace El Rufa’i yayi, sannan zamu kalubalanci sakamakon zaben a gaban kotu, inji Mai Rakumi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.