GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Kashi 6 Cikin 10 Na Matan Ƙasar Nan, Su Na Fama Da Taɓin Hankali – Masana

Kashi 6 Cikin 10 Na Matan Ƙasar Nan, Su Na Fama Da Taɓin Hankali - Masana

76

- Advertisement -

Wani malamin jami’a, Dr Auwal Sani Salihu, yace kashi 6 cikin 10 na mata, da kuma kaso 4 cikin goma na maza a faɗin ƙasar nan su na da taɓin hankali.

 

Karanta: Siyasar Kano: An Kama Wasu Mata Masu Bi Gida-Gida Suna Sayan Katin Zabe A Wajen Mata (Hotuna)

 

Dr Auwal ya bayyana hakan ne a wani taron bita da asibitin kula da ƙwaƙwalwa na gwamnatin tarayya da ke jihar Sokoto ya shirya. Ya ƙara da cewa babban abinda yake kawo tabin hankali shi ne mu’amala da miyagun kwayoyi.

 

Karanta: Ba Mu Kama Mataimakin Gwamnan Kano Ba, Kuma Ba Mu Tsare Shi Ba – Inji DSP Haruna

 

Tun da farko dai Dakta Auwal Sani malamine a jami’ar Bayero da ke Kano, ya ƙara da cewa, akwai cututtuka sama da 300 masu alaƙa da ciwon hauka, waɗanda ka iya kasancewa sun zo da sauki, tsaka-tsaki ko ma su zo da ƙarfin gaske.

 

“Kaso 80 sune ke zuwa da sauki, 20 kuma masu tsananin gaske.”

 

Karanta: Asiri: An Gano Sunan Gwamna El-rufai Kulle Cikin Likkafani A Makabarta (Hotuna)

 

A ƙarshe Dr Auwal ya bayyana cewa, ciwon hauka ba ciwo bane dauwamamme domin akan magance shi an samu kulawa mai kyau.

Leave A Reply

Your email address will not be published.