GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Kayan Shan Ruwan Azumi: Yadda Ake Lemo Daban-Daban Masu Dan Karen Dadi

Kayan Shan Ruwan Azumi: Yadda Ake Lemo Daban-Daban Masu Dan Karen Dadi

407

- Advertisement -

Uwargida a nan bangaren ne za ki taka irin na ki rawan musamman wajen hada kayayyakin makulashe masu dauke da sinadarai masu gina jiki wanda zai taimakawa maigida da yaran gida idan an yi bude baki kari ma hadda ke a ci. A yau za mu nuna ma ki yadda za ki hada kayayyakin lemu daban daban masu dan karen dadi.

 

Karanta: RAMADAN: Addu’ar Yin Bude Baki

 

Watan Ramadana wata ne wanda mafi yawanci mutane na bukatar ci da shan abinci masu kunshe da sinadarai masu gina jiki, sannan masana sun bayyana cewa yana da kyau dan Adam ya ci kayayyakin itace da bude baki tare da yawaita shan ruwa domin ya maye gurbin ruwan da bai sha ba da rana a lokacin da ya ke azumi.

 • GINGER OF ORANGE JUICE
 • GUAVA JUICE
 • MILK SHAKE
 • PINEAPPLE AND YOGHURT ICE
 • BREAK FAST NOG
 • TAMARING JUICE
 • ICED TEA
 • PINACOLADO
 • FRUIT SALAD
 • FRUIT DRINK
 • CHAPMAN
 • BANANA MUSHAKE
 • COCONUT JUICE
 • MIRINDER JUICE
 • MELON BASKET
 • MELON JUICE WITH MILK
 • CARROT DRINK
 • GINGER OF ORANGE JUICE

Abubuwan Da Ake Bukata

 1. Kayan hadi
 2. Citta danya
 3. Leman zaki
 4. Suger
 5. Flavour

Yadda Ake Hadawa
– Bare bayan citta wanke idan angama sai a markada a blender,tace ajiye gefe daya.matse lemo da juice mider idan angama sai a zuba wannan cittar a ciki zuba kankara da flavour.za’a sha da sanyi.

 

Karanta: RIKICIN SARAUTA: Dan Majalisa Ya Maka Masarautar Gwandu A Kotu

 

LEMUN CITTA (GUAVA OF GINGER JUICE)
Kayan hadi:-

•Citta danya
•Gova
•Kanunfari
•Leman zaki
•Suger
•Flavour

Yadda Ake Hadawa
– Dafa suger da kanunfari tace ajiye gefe daya.bare bayan citta wanke sai a markada a jiye gefe daya.markada gova sai a tace,zuba gova da citta,leman zaki a kwano juya kara suger da flavour zuba kankara.a sha da sanyi.

MILK SHAKE
Kayan hadi:-

•Oval tine or milo
•Flavor
•Suger
•Madara

 

Yadda Ake Hadawa

– Zuba madarar gari a kwano zuba milo ko ovaltine,zuba ruwa sai a kada shi sosai har yayi kumfa,zuba kankara da suger dai dai bakinka.zuba a jug.idan anga ya kwanta sai akara juyashi.

LEMUN ABARBA DA NONO (PINEAPPLE AND YOGURT ICE)
Kayan hadi:-

•Abarba
•Yoghurt
•Flavor
•Suger

 

Karanta: Mayakan Boko Haram Sun Kwashi Kashinsu A Hannu A Wata Gwabzawa Da Suka Yi Da Sojoji

 

Yadda Ake Hadawa

-Yanka abarba markada a blender,tace zuba a kwano,zuba yoghurt akai da flavour,suger da kuma kankara,za’a sha da sanyi.

LEMUN KARYA KUMALLO (BREAK FAST NOG)
Kayan hadi:-

•Madara
•leman zaki
•yoghurt
•nutmeg
•ayaba
•suger

 

Yadda Ake Hadawa
– Zuba leman zaki,ayaba,madara da yoghurt a cikin blender idan sun markadu sosai juye a jug,za’a sa a frig(Refrigerator) ko a zuba kankara,zuba nutmeg akai idan kanaso.

 

LEMUN TSAMIYYA (TAMARIN JUICE)
Kayan hadi:-

•Tsamiya
•Suger
•Kanunfari
•Citta
•leman tsami

 

Yadda Ake Hadawa

– Dafa suger da ruwa barshi ya huce.dafa tsamiya da ruwa,kanunfari da citta har misalin minti 30.tace tsamiyar abarshi ya huce yayi sanyi.

Matse leman tsami a kuma yanka guda biyu yankan fadi.hada dafaffan suger acikin tsamiya zuba leman tsami da kuma wanda aka yanka a cikin jug.asaka cikin frig(Refrigerator) yayi sanyi sosai kafin sha.zaka zuba ruwa dai dai tsamin da kakeso kafin sha.

LEMUN SHAYI MAI SANYI (ICE TEA)
Kayan hadi:-

•Ganyan shayi
•Suger
•Leman tsami
•Na’a-na’a
•Kanunfari

 

Yadda Ake Hadawa

– Za’a dafa duka kayan amma banda suger da leman tsami.dafa suger da ruwa.matse leman tsami a kofi ajiye gefe daya.

Tace ganyan shayi da rariya, zuba suger da leman tsami.  Saka cikin firijin(Refrigerator) yayi sanyi sosai.

Idan za’a sha saka ganyan na’a-na’a da aka tsinka guda biyar a ciki da leman tsamin da aka yanka akekkewayo a ciki.a kuma dauki slice daya a yanka bakinsa kadan a saka ajikin bakin kofin. Za’a sha da strew.

 

 

Karanta: Na Kammala Tsara Kunshin Mutanen Da Za Su Kasance Ministocina – Buhari

 

LEMUN KWAKWA DA ABARBA (PINACOLADO)
Kayan hadi:-

•Kwakwa
•Abarba ko leman zaki
•Suger
•Flavour na abarba

Yadda Ake Hadawa

-Za’a goga kwakwa da abun goga kubewa,markada a blender sai a zuba ruwan sanyi a tace da rariya.markada abarba ko [leman zaki] taceta zuba a kwano.dafa suger da ruwa barshi ya huce.

Hada kwakwa da abarba guri daya ko leman zaki zuba suger da flavour juya sosai asa a frig(Refrigerator) yayi sanyi.

wannan leman ana hadashi ne lokacin da za’a sha.idan kuma aka hada aka sa shi a frig(Refrigerator) za’a ga man kwakwar ya taso,ba lalace wa yayi ba sai akara markadawa.

FURUT SALAD (FRUIT SALAD)
Kayan hadi:-

•Abarba
•Gwanda
•Ayaba
•Kankana
•Leman zaki
•Kwakwa
•Leman tsami
•Suger

Yadda Ake Hadawa

-Za’a yanka duk kayan marmarin kanana-kanana(cubes). Za’a bare leman zaki sala-sala sannan acire kwallon a zubar,a tara totuwar leman da ruwan leman a kofi.

Goga kwakwa kanana. Matse leman tsami a kwano,yanka ayaba kanana-kanana sai a zuba cikin leman tsami (yin haka yana hana ayabar tayi baki).

Dafa suger da ruwa ajiye gefe daya. Za’a hada duka yankakkun kayan marmarin waje daya acikin abun da ake hada fruit salad.zuba suger aciki juya sosai.

Idan za’a sha zaka iya zuba condensed milk akan fruits din.

 

 

Karanta: Ayyukar Ibadah Da Ake So A Yawaita Yin Su A Ramadan

 

LEMUN KAYAYYAKIN LEMUN (FRUIT DRINK)

Za’ayi amfani da duka kayan marmarin da muka yi amfani da su a sama.

Za’a zuba a cikin blender a markada su.

Tace da rariya mai laushi (kara ruwa idan kina bukata).

Zuba suger yadda kakeso ( Idan kina da bukata zuba masa madara).

Leave A Reply

Your email address will not be published.