GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Kisa: Uwargida Ta Dabawa Maigidanta Wuka Sau 35 Don Yayi Magana A Kan Rashin Gishiri Girkinta (Hotuna)

Kisa: Uwargida Ta Dabawa Maigidanta Wuka Sau 35 Don Yayi Magana A Kan Rashin Gishiri Girkinta (Hotuna)

27

- Advertisement -

Wata mata ta dabawa maigidanta wuka sau 35 a kan kawai ya kalubalanci girkinta, inji hukumomin kasar Rasha.

 

Maigidan, Slava Davydkin, dan shekaru 43, yaya gunaguni ga matarsa, Evgenia ‘yar shekaru 31, a kan cewa abincin da ta girka masu bai ji gishiri ba a yayin da suka yi baki a gidansu da ke yankin Penza.

 

Karanta: Sojoji Sun Fafata Da Mayakan Boko Haram A Garin Rann

 

Bayan da mijin na ta ya mata gunaguni, Evgenia sai da ta jira maigidan na ta na bacci sannan ta daba masa wuka har lahira a gaban dansu dan shekaru 4, inji rahotanni.

 

Daga baya ta furta aikata laifin da ake zarginta da shi. An garkame ta.

 

Karanta: Wuta Ya Lashe Motocin Kamfen Na Jam’iyyar PDP

 

An samu labarin cewa ma’auratan sun dan yi fada a tsakaninsy bayan Slava yayin gunaguni a kan garkin matarsa. Inda ya ce hakan ya nuna cewa ba ta sonsa, Ma’auratan sun ci gaba da fada a tsakaninsu bayan da bakinsu suka kwanta inda uwargidan Slava ta bayyana cewa maigidan na ta ya ma ta duka.

 

Evgenia ta fadawa ‘yan sanda cewa mijin na ta ya bata ma ta rai bayan sun ci abinci da ruwan giya, shi ya sa suka daba masa wuka. Sai ta tada bakon na su ta fada masa ya kira ma ta bas din asibiti.

 

Karanta: Tsafi: An Kama Wani Matashi Yayi Shigar Mata Tare Da Jakka Makil Da Kamfen Mata (Hotuna)

 

Ma’aikata kiwon laifya na asibiti suka tabbatar da mutuwar maigidan na ta a nan take.

 

Ga hotunan ma’auratan a kasa;

Maigidan matar, Slava

Wukar da matar ta yi amfani da shi wajen kashe maigidanta

  Slava tare da Evgenia

Leave A Reply

Your email address will not be published.