GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Kisan Janar Alkali: ‘Yan Sanda Sun Cafke Matar Da Ta Jagoranci Zanga-Zangar Hana Yashe Kogin ‘Dura-Du’

Kisan Janar Alkali: 'Yan Sanda Sun Cafke Matar Da Ta Jagoranci Zanga-Zangar Hana Yashe Kogin ‘Dura-Du’

21

- Advertisement -

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato sun bayyana kama mutane 19 wadanda ke da hannu dumu dumu a kisan marigayi Janar Idris Alkali ciki har da matar da ta jagoranci zanga-zangar mata sanye da bakaken kaya don hana yashe kogin ‘Dura Du’ inda aka gano motar marigayin da wasu kayan sawansa.

 

Karanta wannan: Shekaru Ko Tsufa Bai Hana Saduwa Tsakanin Namiji Da Mace Sai Dai Idan Mutum Raggo Ne – Binciken Masana

 

Rundunar dai ta kama Rebecca wacce matar mai anguwar Latiya ne a yankin Du ami da wani Pam Gyang Dung wanda ke cikin ainihin mutanen da suka hallaka Janar Idris Alkali.

 

Karanta wannan: Mafi Karancin Albashi: Kungiyar NUPENG Tana Tattauna Kan Ko Zata Shiga Yajin Aiki

 

Kazalika rundunar na rike da Stephen Chuwang da ya amsa ya na daga cikin wadanda su ka sauyawa gawar Idris Alkali waje daga ramin da suka sanya shi zuwa wata tsohuwar rijiya a Guchwet.

 

Karanta wannan: Zaben 2019: Ezekwesili Ta Yi Ganawar Sirri Da I.B.B

 

Jami’in labarun rundunar ‘yan sandan na Filato Tyopez Terma ya ce zasu gurfanar da mutanen a gaban kotu bisa ga irin rawar da kowanensu ya taka a kisan Janar din.

Leave A Reply

Your email address will not be published.