GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Kotu Ta Tabbatar Da Hon. Abdullahi A Matsayin Dan Takarar Majalisar Wakilai Na APC

Kotu Ta Tabbatar Da Hon. Abdullahi A Matsayin Dan Takarar Majalisar Wakilai Na APC

519

- Advertisement -

Babbar kotun daukaka kara (Court of Appeal) dake zama a babban birnin tarayya Abuja ta yanke hukunci akan shari’ar Abdullahi Idris Garba da Abdulmalik Sarkin Daji.

 

Karanta: Majalisar Dattawa Ta Amince Da Ware Naira Biliyan 10 Ga Zamfara

 

Kotun ta yanke hukuncin ne a yau alhamis 11/04/2019 inda ta tabbatar da Abdullahi Idris Garba (Maisola) a matsayin wanda yayi nasara a zaben fidda gwani na jam’iyar APC da aka gudanar, kuma wanda ya lashe babban zaben 2019 na kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar yankin Kontagora, Mariga, Mashegu, Wushishi karkashin jam’iyar APC da hukumar zabe ( INEC) ta gudanar.

 

Karanta: Shugaba Buhari Makaryaci Ne – Inji Reno Omokri

 

Tun bayan kammala zaben fidda gwani na kujerar dan majalisar tarayya na yankin Kontagora, Mariga, Mashegu, Wushishi da jam’iyar APC tayi wanda uwar jam’iyar APC ta kasa ta tabbatar nasarar Abdullahi Idris Garba Maisola ake cigaba da samun satoka-sakatsi a tsakanin ‘yan takarar biyu wanda kowani ke ikirarin shine halastaccen dan takarar da yayi nasara inda uwar jam’iyar ta APC ta tura sunan Maisola a matsayin dan takarar ta a babban zaben 2019 da ya gudana, wanda hakan yasa Abdulmalik Sarkin Daji ya garzaya kotu domin tabbatar da sahihancin sa inda babban kotun tarayya dake zama a Minna babban birnin Jihar Neja ta tabbatar da shine dan takarar da yayi nasara a zaben fidda gwani da aka gudanar sakamakon hakan yasa abokin hamayyarsa Abdullahi Idris Garba ya daukaka kara zuwa kotun daukaka kara dake Abuja wanda shima yayi nasara a yau.

Leave A Reply

Your email address will not be published.