GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Kotu Ta Yankewa Matashi Hukuncin Kisa Bisa Kashe Mahaifiyarsa Kan Layar Bata A Jos

Kotu Ta Yankewa Matashi Hukuncin Kisa Bisa Kashe Mahaifiyarsa Kan Layar Bata A Jos

39

- Advertisement -

Wata babbar kotu a garin Jos da ke jihar Filato ta yankewa wani matashi mai kimanin shekaru 20 a duniya mai suna Agugu Adau hukuncin kisa ta hanyar rataya a bisa kama shi da laifin kashe mahaifiyarsa.

 

Alkalin kotun, Justice Nafisa Musa, ta yankewa matashin hukuncin kisan ne bayan da ta tabbatar da matashin ya hallaka mahaifiyarsa har lahira.

 

Karanta: Murnar Lashe Zabe: Zamu Cafke Duk Wanda Aka Kama Yana Tukin Ganganci a Kaduna – ‘Yan Sanda

 

A bisa hujjojin da aka gabatar ga wannan kotun, mai shigar da ƙara ya shaidawa kotun cewar Adau bai ji tausayi ko imanin ba wajen kashe mahaifiyarsa.

 

A ƙarshe mai Shari’a Nafisa ta ce sabo da haka wannan kotun ta yanke maka hukucin kisa ta hanyar rataya har sai ka mutu, Allah ya yi maka sassauci bayan ka koma gareshi.

 

Karanta: Amfanin Ruwan Tumatir A Jikin Dan Adam

 

Tun da farko dai kamfanin dillacin Labarai na ƙasa wato NAN ya rawaito cewar wanda aka yankewa hukuncin ya aikata laifin ne a ranar 30 ga watan Disamban shekarar 2016 inda ya kashe mahaifiyarsa a lokacin da ya bukaci ta bashi ‘Layar’ da yake bayanin mahaifinsa ya mutu ya bar masa, inda ta ki bashi, a bisa wannan dalilin ne ya halakata har lahira kamar yadda ya fadi dalilinsa na kisan nata.

 

Karanta: Mun Kammala Shiri Tsaf Domin Gudanar Da Zaɓen Gwamnoni – INEC

 

Agugu Adau ya aikata wannan mummunan laifin ta’addancin ne a ƙauyen Kisaghyip da ke cikin ƙaramar hukumar Bassa a cikin jihar Filato, a lokacin da suke cikin gona da shi da mahaifiyar tasa

Leave A Reply

Your email address will not be published.