GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Kotu Ta Yankewa Wasu Matasa 4 Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Laifin Sata

Kotu Ta Yankewa Wasu Matasa 4 Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Laifin Sata

36

- Advertisement -

Wata babbar kotu mai zama a garin Asaba babban birnin jihar Delta, ta yankewa wasu mutum hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun su da aikata miyagun laifuka da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane da kwacen mota.

 

Karanta: Uses of Sodom Apple

 

Kotun ta yanke wannan hukuncin ne a cikin wani jawabi na tsawon sa’a hudu da alkalin kotun, Mai Shari’a Flora Azinge, ta karanta a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris inda mai shari’ar ta zartar wa da mutane hudu daga cikin masu laifin da aka gurfanar a gaban ta.

 

Karanta: ‘Babu Gudu Babu Ja Da Baya’ – Inji ‘Yar Shi’an Da Ta Rasa ‘Ya’Ya 5 A Rikicin Zaria

An tuhumi mutum biyar; Uche Uzondu, Emeka Amukali, Paul Egwom, Festus Oghali, da David Mario, da hada baki tare da aikata laifin fashi da makami da garkuwa da mutane inda mai shari’ar ya ware David Mario, daya daga cikin mutane hudu da aka gurfanar saboda rashin hujja mai kwari da ta alakanta shi da laifuka da ake zargin su da aikatawa

Leave A Reply

Your email address will not be published.