GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Ku Tashi Da Azumi Domin Samun Nasarar Gwamna Ganduje – In Ji Faizu Alfindiki

Ku Tashi Da Azumi Domin Samun Nasarar Gwamna Ganduje - In Ji Faizu Alfindiki

81

- Advertisement -

An yi kira ga ɗaukacin magoya bayan gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje a duk inda su ke a faɗin jihar Kano da su tashi da azumi ranar Litinin domin Gandujen ya samu nasarar lashe zaɓen da zai shiga a zagaye na biyu.

 

Karanta: Kotu Ta Yankewa Matashi Hukuncin Kisa Bisa Kashe Mahaifiyarsa Kan Layar Bata A Jos

 

Wannan kiran ya fito ne ta bakin mataimakinsa na musamman akan harkokin yaɗa labarai wato Honarabul Faizu Alfindiki.

 

Tun da farko dai Faizu Alfindiki ya yi wannan kiran ne a shafinsa na fesbuk a safiyar yau ɗin nan.

 

Karanta: Babban Hadimin Ganduje Ya Ajiye Aikinsa Sabo Da Gwamnan Ya Ƙi Karɓar Ƙaddara

 

“Muna Kira ga duk wani Ɗan Gandujiyya da mai kishin Kano da ya tashi da azumi ranar litinin mai zuwa da niyyar Allah ya bamu nasara” In ji Faizu Alfindiki.

 

Karanta: Zaben Kano: Ina Da Tabbacin Samun Nasarar Lashe Zaɓen Da Za’a Sake – In Ji Gwamna Ganduje

 

Idan za’a iya tunawa dai cikin makon da ya gabata ne aka gudanar da zaɓen gwamna a jihar Kano tsakanin gwamna mai ci wato Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC da kuma Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP, wanda hukumar zaɓe ta bayyana sakamakon zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.