GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Kungiyar JIBWIS Ta Horas Da Masu Digiri Marasa Aiki Sana’o’in Dogaro Da Kai

Kungiyar JIBWIS Ta Horas Da Masu Digiri Marasa Aiki Sana'o'in Dogaro Da Kai

21

- Advertisement -

Kungiyar Jama’atu Izaltil Bid’ah Wa’ Ikamatis Sunnah reshen jihar Jigawa ya horas da mata da matasa masu digiri 81 sanaoin dogaro da kai.

 

Karanta: ‘Yan Sanda Sun Cafke Matar Da Ta Kashe Dan Makwabcinta Don Ta Azzabtar Da Shi (Hoto)

Shugaban kungiyar na jiha Malam Abubakar Jibril ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse
Yace sun bada horan ne na tsawon kwanaki hudu a Birnin jiha Dutse

Mallam Jibril Abubakar ya kara da cewar wadanda aka baiwa horan sun hadar da maza 54 da kuma mata 27 da aka zabo daga kananan hukumomin jihar nan 27

 

Karanta: Filin-Ra’ayi:- Jam’iyyar APC Ta Gaza Tun Daga Sama Har Kasa (Kashi Na 1): Cin Hanci Da Rashawa

Yace an horas da maza sanaoin gyaran wayar hannu yayinda aka horas da mata hanyoyin gyaran daki
A cewarsa hakan na daga cikin kudirin kungiyar na marawa gwamnati baya wajen samarda aiyukan yi ga matasa da kuma rage aikata munanan dabiu.

 

Karanta wannan: Abunda Ke Janyo Ciwon Gyambon Ciki (Ulcer) Wanda Mutane Ba Su San Da Shi

Rahotanni na cewar kowanne daga cikinsu ya samu jarin naira dubu goma domin far asana-a

Leave A Reply

Your email address will not be published.