GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Lauyan Atiku Bashi Da Lasisin Shiga Harkokin Shari’a a Najeriya – INEC

Lauyan Atiku Bashi Da Lasisin Shiga Harkokin Shari'a a Najeriya - INEC

35

- Advertisement -

 

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta ce korafin da Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya shigar ba ya da nasaba da sa hannun wani lauya mai lasisin shiga harkokin shari’a a Najeriya.

 

Karanta: Yusuf Tare Da Abokinsa Sun Yi Tattaki Daga Minna Zuwa Abuja Don Taya Hon. Abdullahi Murnar Lashe Zabe (hotuna)

 

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, hukumar INEC ta ce korafin da Atiku ya gabatar a gaban kotun bai samu sa hannu na Lauya mai lasisin shiga harkoki na shari’a a Najeriya ba.

Ko shakka ba bu Atiku wanda ya kasance tsohon shugaban kasar Najeriya ya shigar da korafi a gaban kotun daukaka kara domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Atiku yayin hawa kujerar naki ta amincewa da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari, na ci gaba da neman hakkin sa a shari’ance in da lauyoyi kimanin 32 ke wakiltar sa bisa jagorancin wani zakakurin Lauya, Livy Uzoukwu.

 

Karanta: Kotu Ta Yankewa Wani Dan Luwadi Hukuncin Dauren Wata Daya Bayan Ya Turmushe Yaro Dan Shekaru 12 Har Lahira

 

Sai dai cikin mayar da martanin tuhumar da ke kanta, hukumar INEC ta ce Lauyan Atiku baya da cancantar shiga al’amura na shari’a a Najeriya sakamakon rashin samun lasisi wakilci na shari’a daga kotun koli ta kasar nan.

Yayin ganawar ta da manema labarai a watan Maris da ya gabata, tawagar lauyoyi masu kare Atiku ta yi furuci na samun wadatattun hujjoji gami da dalilai na kalubalantar sakamakon zaben kujerar shugaban kasa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.